Gwamnonin Najeriya sun amince su sanya dokar ta-baci a kan matsalar fyade da cin zarafi musamman wanda ake wa mata da kananan yara.
Gwamnonin sun kuma jaddada aniyarsu ta tabbatar da ganin masu fyade da sauran masu cin zarafa mai alaka da jinsi sun fuskanci hukunci daidai da girman laifinsu.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya sanar da haka a takardar bayan taronsu na ranar Laraba.
Taron ya kuma bukaci dukkan gwamnoni su hanzarta tabbatar da jihohinsu na amfani da dokokin kare raunana da kananan yara da mata da kuma hukunta masu aikta laifukan cin zarafi na jinsi.
Kungiyar na kuma neman a hanzarta wurin gudanar da bincike, gurfanarwa da hukunta masu fyade tare da sanya sunayensu a rajistar masu kazamar dabi’ar domin kunyata su da zama darasi.