Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta sako wani dan kasar Faransa ta ke tsare a hannunta, bayan da dangantaka ya kara tsami tsakanin kasashen biyu.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa, ta bayyana jin dadinta a safiyar Alhamis da sakin Stephane Jullien, wanda gwamnatin sojin Nijar ta tsare shi bayan da jijiyoyin wuya suka tashi tsakanin kasashen biyu.
- An haramta wa jiragen ruwa tafiyar dare a Taraba
- NAJERIYA A YAU: Yadda Matsin Rayuwa Ke Shafar Karatu A Najeriya
A ranar Talata Faransa ta yi korafi game da tsare Jullien tun ranar Juma’a da ta gabata, tana mai kira da a sako shi.
Jullien, dan kasuwar Faransa ne mazaunin Nijar kuma wakiltin ’yan kasarsa a ofishin jakadancinta da ke birnin Yamai.
Dangantakar Faransa da Nijar ta yi tsami ne tun bayan da sojoji suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli, wanda babban abokin kasar Turawan ne.
Faransa na da sojoji 1,500 da ta girke a Nijar domin yakar ’yan bindiga masu ikirarin jihadi a yankin Sahel, inda ta tsaya kai da fata wajen taimakon gwamnatin Bazoum ta wannan fuska.
Ta ayyana gwamnatin sojin Nijar a matsayin haramtacciya, ita kuma gwamnatin sojin ke neman sojojin turawan su kwashe kayansu daga kasar.
A makon jiya dai, rundunar sojin Faransa ta ce ta fara tattaunawa da sojojin Nijar kan batun janye sojojin Faransa daga kasar.