✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta

An ɗora wa tawagar alhakin binciko haƙiƙanin abin da ya faru, tare da hana faruwar hakan a gaba.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunkure.

“Manufarmu a bayyane take – bincike, tattaunawa da bayar da shawarwari masu ɗorewa.

“Wannan ba kawai yawon neman gaskiya ba ne, har ila yau ƙoƙari ne na kawo zaman lafiya, domin hana sake faruwar irin wannan tashin hankali,” in ji mataimakin gwamnan

Tawagar za ta gana da Gwamnan Jihar Edo, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin fararen hula domin fahimtar matsalar tare da kawo hanyoyin sasanci.

Gwarzo, ya ce tawagar za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an samun zaman lafiya da hana faruwar irin wannan rikici a gaba.

Wannan ƙoƙari na cikin shirin Gwamnonin Arewa na haɗin kai da goyon bayan zaman lafiya a faɗin Najeriya sakamakon ƙaruwar rashin tsaro da ake fuskanta.

“Wannan shiri wani ɓangare ne na matakan haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa domin nuna goyon baya, haɗin kai a ƙasa da kuma tunkarar matsalar tsaro da ke ƙaruwa a sassa daban-daban na Najeriya,” in ji shi.