Gwamnan Kebbi Nasiru Idris ya rushe shugabannin riko na daukacin kananan hukumomi da ke Jihar.
Sanarwar da Mukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu na jihar, Aliyu Hassan Kalgo ya fitar ta ce rushe kantomomin ya fara aiki ne nan take.
Sanarwar da aka fitar a madadin kwamishinan ma’aikatar, ta umarci rusassun kantomomin sun mika ragamar gudanar da ofisoshinsu da daraktocin gudanarwar kananan hukumominsu.
Gwamnan ya nada kantomin ne bayan karewar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar a watan Fabrairun shekarar 2023 da ta gabata.
- Sau 8 aka aura min ’yan Boko Haram —Ɗalibar Chibok Mai Juna-biyu
- An gano gawarwakin ’yan bindiga 8 a dajin Kaduna
- Man dizel din Matatar Dangote ya fi wanda ake shigo da shi inganci —Majalisa
Rushe kanomomin ba zai rasa nasaba da da hukuncin Kotun Koli da ya ba wa kananan hukumomin ’yancin cin gashin kansu.
Bayan hukuncin ne jam’iyyun adawa da kungiyar (IPAC ) suka bukaci a rushe kantomimin, kasancewar hukumar zaben jihar (KESIEC) ta shirya gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi ranar 31 ga watan Agusta mai kawama.