Gidauniyar Zakka da Wakafi ta Jihar Gombe ta horar da matasa 370 dabarun dogaro da kai a tsawon shekaru hudun da suka gabata.
Horon na shekara-shekara an fara shi ne a shekarar 2020 zuwa wannan shekarar 2023, inda aka bai wa matasa maza da mata horon da ba sai sun dogara da aikin gwamnati ba.
Bayanai sun ce kawo yanzu dai matasan sun yi nisa a sana’o’in da suka koya wajen neman na abinci.
A zantawarsa da wakilinmu bayan kammala taron, Shugaban Gidauniyar, Dokta Abdullahi Abubakar Lamido, ya bayyana cewa makasudin wannan taro shi ne koyawa matasan dabarun zaman rayuwa kan yadda za su koyi dogara da kansu ta hanyoyi daban-daban bayan kammala karatun su.
Dokta Abdullahi Lamido, ya kara da cewa matasan da suka ci moriyar horon sun gano cewa suna da wata baiwar yadda za su tafiyar da rayuwarsu ba tare da sun sani ba.
Ya ce cikin wadanda suka amfana da horon a rukuni na biyu an samu wanda a halin yanzu yana iya samarwa da kansa naira dubu 18 duk wata, wanda shi ne mafi karancin albashin da gwamnati ke iya biyan ma’aikata.
Ya ce “matashin wanda a halin yanzu dan makaranta ne ina kuma ga idan ya kammala karatu ya maida hankali kan sana’ar sosai.
“kididdiga ta nuna cewa a Jihar Gombe ana da mutum miliyan 3.5 wanda a cikin su masu aikin gwamnati a dukkan matakai ba su wuce kashi 1.4 ba.
“Lallai idan haka ne dole a tashi tsaye wajen ganin an samu mafita,” inji shi.
Ya ce idan mutum ya samu yadda zai yi ya gina sana’arsa zai zama mai bada aiki ne ga wasu ba mai neman aiki ba wanda yin hakan ya zama cewa ya taimaki kansa da ma wasu.
Kazalika, ya shawarci matasan da cewa su mayar da hankali kan abin da ake koya musu saboda ya amfane su da sauran al’umma.
Wasu mahalarta taron da muka zanta da su sun nuna jin dadin su ga gidauniyar ta zakka da wakafi bisa ilimin da ta ba su na samun abin dogaro a rayuwar su da a baya ba su da masaniya a kai.
Sun bayyana cewa “tun ba a gama ba ma mun gane ashe ba aikin gwamnati ne kadai ke samarwa da mutum yadda zai yi rayuwa da sana’a ko kasuwanci ba.”