✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama matashi kan zargin luwadi da dan shekara 4 a Gombe

An kuma kama wasu mutum 4 da suka kware wajen ta’adar sace-sace a gidajen jama’a.

An kama wani matashi da ake zargi da aikata luwadi da wani karamin yaro dan shekara hudu a Karamar Hukumar Balanga ta Jihar Gombe.

Bayanai sun ce wasu kwararrun mafarauta ne suka cafke mutumin da ake zargi a karamar hukumar.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa mafarautan sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da jama’a ke kokarin daukar doka a hannunsu bayan kama shi da aka yi dumu-dumu yana luwadi da yaron.

Mahid, ya ce da misalin karfe 8 na dare ne aka kama wanda ake zargin, wanda kuma aka mika wa jami’an ’yan sanda domin daukar matakin da ya dace.

Kakakin ’yan sandan ya ce an garzaya da yaron asibitin domin duba lafiyarsa, a yayin da ’yan sanda ke ci gaba da gudanar da binciki domin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Kazalika, ASP Mahid ya ce rundunar ’yan sandan ta kama wasu mutum 4 mazauna unguwar London mai Dorawa da suka kware wajen ta’adar sace-sace a gidajen jama’a a Gombe.

Kakakin rundunar ’yan sandan ya ce a ranar 14 ga watan Nuwamba ne jami’an hadin guiwa na Operation Hattara suka kama su a wani lokacin da suke sintiri a unguwar.

Ya ce barayin sun fasa gidaje biyar a unguwar Zagaina, inda suka yi nasarar sace babura 6 a lokuta daban daban.

A cewarsa, bincike ya yi zurfi a kan lamarin kuma da zarar sun kammala za su tura su zuwa kotu domin su fuskanci hukunci.

%d bloggers like this: