✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ɓarayin babura a Gombe

Baburan sun haɗa da Qlink Cassie mai lamba ABC 484 WN da Hero Hunter mai lamba GME 36 QL.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da satar abun hawa wadanda ta ƙwato babura biyu a hannunsu hadi da wani wanda aka tsinta a lokacin sintiri.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an gudanar da samamen ne bisa bayanan sirrin da aka samu daga wani mai kishin ƙasa, wanda ya kai jami’an Operation Hattara har zuwa wata maɓoyar ɓata gari a Tudun Hayin Kwarin-Misau, da ke yankin Ƙaramar Hukumar Akko

Rundunar ta ce an kama Misba’u Adamu mai shekaru 25 dan asalin garin Alkaleri na Jihar Bauchi da Adamu Ibrahim mai shekaru 28, daga Karamar Hukumar Garko ta Jihar Kano.

A lokacin binciken, waɗanda ake zargin sun amsa laifin satar babura guda biyu a gidan wani Mohammed Usman da misalin karfe 4 na Asuba a ranar 6 ga Yuli, 2025.

Baburan sun haɗa da Qlink Cassie mai lamba ABC 484 WN da Hero Hunter mai lamba GME 36 QL.

A sanarwar, rundunar ’yan sandan ta kiyasta darajar baburan kan Naira miliyan 1.8 wadanda aka gano a gidan wani abokin huldarsu da ake kira Babangida.

A wani labarin na daban, rundunar ta ce wani mutum ya tsere ya bar babur kirar Jincheng Kasea mai lamba DKU 099 UK a Wuro Birji yayin da ‘yan sanda ke sintiri da misalin karfe 1 na dare.

Rundunar ta ce tana ci gaba da kokarin gano masu laifin da kuma mamallakin babur ɗin da aka tsinta.

Ta kuma jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da kira da su ci gaba da ba da bayanai masu amfani.