✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutane 1,611 da ƙwato motoci 21, babura 51 da aka sace a Abuja

Shida daga cikin motoci 21 da aka ƙwato an mayar wa masu su bayan an tantance su, yayin da sauran motocin 13 ke nan a…

Rundunar ’yan sandan birnin tarayya Abuja ta ce ta kama mutane 1,611 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da safarar miyagun ƙwayoyi tare da ƙwato motocin sata guda 21, babura 51 da kuma miyagun ƙwayoyi.

Kwamishinan ’Yan sanda CP Ajoa Saka Adewale, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da motocin da aka ƙwato, baburan da sauran kayayyaki a gaban manema labarai a ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce an kama mutane 16 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban na satar mota. Ya kuma ce shida daga cikin motoci 21 da aka ƙwato an mayar wa masu su bayan an tantance su, yayin da sauran motocin 13 ke nan a hannun rundunar.

Ya ce, rundunar ta kai samame da dama a wurare da dama, inda ta kama mutane 1,611 da ake zargi, inda ya ce da yawa daga cikinsu na da alaƙa da laifukan da suka shafi muggan ƙwayoyi da sauran miyagun ayyuka.

Adewale ya ce, an gano wasu adadi mai yawa na miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi a yayin gudanar da samamen, waɗanda a halin yanzu ake tsare da su a matsayin baje kolin da za a ci gaba da gudanar da bincike da kuma gurfanar da su gaban ƙuliya.