Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo.
Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu.
- An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun
- NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya
Ana zargin al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, amma ba a samu cikakken bayani ba sai zuwa ranar Lahadi.
Wani mazaunin Ifon, wani gari da ke iyaka da Jihar Edo, ya shaida wa Aminiya cewa mutuwar matashin ta sa al’umma da abokansa yin bore.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne tun a ranar masoya.
Samun labarin mutuwar matashin ke da wuya, sai matasan suka ɗunguma zuwa ofishin ’yan sanda..
Ya ce ’yan sandan sun kasa shawo kan masu boren da suka mamaye ofishin, inda suka banka masa wuta a fusace.
Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin.
Ta kuma ƙara da cewa Kwamishinan ’yan sandan jihar, Wilfred Afolabi, na kan hanyarsa ta zuwa Ifon domin ta tabbatar da zaman lafiya da kuma hana sake aukuwar wani tashin hankali.