✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EU za ta ba wa mata da yara tallafin N116bn a Afghanistan

EU za ta ba da kudin ne bayan da ta samu tabbaci daga Taliban cewa mata da kananan yara za su amfana

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta amince ta ba wa kasar Afghanistan tallafin Yuro miliyan 140 — kimanin Naira biliyan 116 — domin mata da kananan yara.

EU za ta ba da kudin ne daga asusunn tallafin da ta ware wa Afghanistan, bayan da ta samu tabbaci daga Taliban cewa mata da kananan yara za su samu tallafin.

Yuro miliyan 140 din wani kaso ne daga tallafin Dala biyan guda da EU ta ware wa Afghanistan a watan Agustan 2021, wanda daga ciki an riga an fitar da Yuro miliyan 980.

Bayan dawowar mulkin Taliban a watan Agustan 2022, EU ta rufe asusun ajiyar kasar a watan Disamba kan zargin kungiyar da sanya tsauraran dokoki da ke tauye hakkin mata.

Hakan ta faru ne bayan Taliban ta umarci kungiyoyin cikin gida da na kasashen waje da ke aiki a Afghanistan da su sallami ma’aikatansu mata.

Amma bayan wata shida Hukumar EU ta yanke shawarar sakin kudaden bayan ta samu tabbacin gwamnatin cewa tallafin zai isa ga mata da kananan yara.

Tarayyar ta ce za ta ba ta kudaden ne ta hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya da kuma kungiyoyin jinkai na kasa da kasa da ke aiki a Afghanistan.

A watan Fabrairu ne ta amince da ci gaba da ba da tallafin, bisa sharadin tallafin ya kasance a bangarorin da mata za su amfana.

A watan Yuli Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Afghanistan ya sanar cewa mutum miliyan 24.4 a kasar na bukatar agajin jinkai a kasar.

Ana sa ran kudaden da EU za ta saki za su taimaka wajen samar da muhamman abubuwar rayuwa ga al’ummar Afghanistan, da kuma tallafi ga wadanda suka tsere zuwa makwabta.

A baya Majalisar Dinkin Duniya ta sanar cewa tun bayan takunkumin da aka sanya, Taliban ke kokarin aiki da kungiyoyin kasa da kasa kan yadda za su yi aiki a kasar.

Wasu daga cikin kungiyoyin har sun ci gaba da aiki a lardnan da suka cim-ma yarjejeniya da gwamnatocin yankin, musamman a bangare kiwo lafiya.