Mutane da dama sun rasu, wasu dubbai kuma suka tsere daga gidajensu a sakamakon harin da ’yan bindiga suka kai wasu yankuna bakwai da ke kan iyakar Jihar Kebbi da maƙwabciyarta Jihar Sakkwato.
A yayin ƙazamin harin, ’yan bindigar sun rika kashe-kashe suna cimma wa gidaje da shaguna da dama wuta, lamarin da ya sa mazauna yankunan, waɗanda akasarinsu manoma ne gudun neman tsira.
- An cafke likitoci 2 kan satar ƙodar mara lafiya a Jos
- NAJERIYA A YAU: Shin Matasa Sun Gamsu Da Ministocin Da Ake Son Naɗa Musu?
Yankunan da aka kai harin su haɗa da Zawaini, Jangargari, Jaja da ke ɓangaren Jihar Kebbi, sai kuma ƙauyen Karani da wasu uku a ɓangaren Jihar Sakkwato.
Majiyarmu ta ce dubban mazauna yankunan ne suka tsere zuwa yankin Jarkuka da ke Karamar Hukumar Arewa ta Jihar Kebbi, inda suka samu mafaka.
Majiyar ta ci gaba da cewa waɗanda harin ya tilasta wa tserewa daga ƙauyukansu sun rika roƙon mazauna domin samun abinci da wurin kwana.
A kan haka ne Gwamnatin Jihar Kebbi ta ba da umarnin rabon kayan tallafi ga ’yan gudun hijirar.
Wani jami’in gwamnati ya shaida wa wakilinmu cewa Gwamna Nasiru Idris ya tura Kwamishinan Yada Labarai, Yakubu Ahmed Birnin Kebbi tare a Kwamishinan Jinƙai, Muhammad Hamidu Jarkuka suka kai wa mutanen ziyarar jaje da kuma kayan tallafi da suka hada da hatsi da kayan masarufi da shimfidu da sauransu.
An yi rabon kayan ne bisa kulawar sarakunan gargajiya da kuma shugaban Karamar Hukumar Arewa Alhaji Sani Aliyu Tela Kangiwa.