Gwamnatin Jihar Kano ta dora laifin mutuwar daliban Islamiyya 20 a hatsarin jirgin ruwa a yankin Bagwai a kan daukar kaya fiye da kima.
A sakon ta’aziyyarsa, Gwamna Abdullahi Ganduje, ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga jihar, sannan ya roki Allah Ya jikan mamatan da kuma samun sauki ga wadanda suka samu rauni.
- Daliban Islamiyya 20 sun rasu a hatsarin kwalekwale a Kano
- Daliba ta bude shafin koyar da Lissafi da harshen Hausa
Ya bayyana cewa, “Zuwa safiyar Laraba, an tabbatar da rasuwar mutum 20, mutum bakwai suna kwance a asibiti, sannan an gano karin mutum takwas a safiyar, a yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto.”
Sanarwar da kakakinsa, Abba Anwar ya fitar ta gargadi masu kwalekwale da su guji daukar mutane da kaya fiye da kima, wanda shi ne dalilin kifewar jirgin ruwan, domin “ba sai sun yi lodi fiye da kima ba za su samu riba.”
“Mun gano cewa jirgin ya taso daga Hayin Badau zuwa Bagwai, ya dauko mutum kusan 50, yawancinsu daliban Islamiyya ne da za su je taron Mauludi, da kuma kaya, amma ya kife saboda lodin ya wuce kima,” inji shi.
Ganduje ya tuno da wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya ritsa da mutane da dama a Bagwai a shekarun baya, yana mai cewa, “Ya kamata mutane su dauki ransu da na sauran mutane da muhimmanci, ta yadda ba za su rika yin kasada da su ba.