Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta Babbar Kotun ta Jihar Kano ta ce za ta yanke hukunci nan gaba a shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, da matarsa Hafsat, da wasu mutane da kamfanoni shida.
Gwamnatin Jihar Kano ta tuhumi waɗannan mutane da kamfanoni da laifuka guda takwas da suka haɗa da karɓar rashawa, yin amfani da kuɗin jama’a ta haramtacciyar hanya, da kuma satar kuɗin gwamnati.
Ganduje ya yi gwamnan Jihar Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Lauyan Ganduje ya roki kotu da ta ba shi karin lokaci a shari’ar amma lauyan gwamnati ya soke wannan roko kuma ya bukaci kotu da ta yi watsi da shi.
- Ka dawo Najeriya ka magance matsalar tsaro —Obi ga Tinubu
- Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan jarida su daina kawo rahoton ayyukan ’yan ta’adda
- Hisbah ta kama matashi yana ‘lalata’ da Akuya a Kano
Lauyoyin wasu mutane da kamfanoni da ake tuhuma a shari’ar sun kuma gabatar da wasu batutuwa kuma sun roki kotu da ta na su gaskiya tare da umartar gwamnati da ta biya su diyya.
Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta dakatar da sauraron ƙarar kuma ta ce za ta sanar da dukkan waɗanda abin ya shafa ranar da za ta yanke hukuncinta daga baya.