Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci zauren Majalisar Wakilai a ranar Alhamis domin ganewa idanunsa ficewar wasu mambobi biyu na Jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
’Yan majalisar biyu, sun haɗa da: Dan Majalisar Wakilai, Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar mazaɓar Rogo/Karaye da kuma Ɗan Majalisar Wakilai Kabiru Alhassan Rurum mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Rano/Bunkure/Kibiya, sun sauya sheƙa a ranar Alhamis.
- Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato
- Dalilin da ya sa gwamna Bala ya yi ƙoƙarin mari na – In ji Minista
Hakazalika mamba mai wakiltar mazaɓar Ijesha Oriade/Obokun na Jihar Osun, Wole Oke, ya kuma bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC.
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudden Abbas wanda ya sanar da sauya sheƙar, ya bayyana cewa mambobin sun bayyana dalilansu na ficewa daga jam’iyyarsu zuwa APC.
Sai dai Babban mai tsawatarwa na Marasa Rinjaye, Isa Ali JC, ya nuna rashin amincewarsa da cewa sauya sheƙar ya sabawa kundin tsarin mulkin ƙasar.
Ganduje wanda ya samu rakiyar wasu jami’an jam’iyyar, ya fice bayan sanarwar.