Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce APC ba ta girgiza ba, kuma ta mayar da hankali ne kan karfafa madafunta.
A cikin wani bidiyo, a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan bayan ya jagoranci masu ruwa da tsaki na APC zuwa ganawa da Buhari a gidansa, Ganduje ya ce sun ziyarci Buhari ne don sanar da shi irin nasarorin ci da jam’iyyar ta samu tun bayan barinsa mulki da kuma tabbatar da kudirinsu na tabbatar da ci-gaban ayyukansa.
“Ba mu ba damu ko kadan. Mun zo ne don girmama tsohon shugaban kasa kuma mu sanar da shi nasarorin da babbar jam’iyyarmu ta samu tun bayan saukarsa daga mulki. Mun tabbatar masa da cewa za mu ci gaba da sanar da shi ina aka kwana akai-akai game da halin da ake ciki,” in ji Ganduje.
Game da ziyarar Atiku ga Buhari, wadda ake gani a matsayin yiwuwar haɗewarsu a siyasa, Ganduje ya yi watsi da ita a matsayin mara muhimmanci.
“Wannan ziyarar ba ta dame mu ba. Ƙoƙari ne maimaita tarihi amma abin da suke nema ba zai yiwu ba. Abin da suke kokarin ginawa ba shi da tushe. Wasu ɓangarorin ba za su taɓa iya haɗuwa ba,” in ji shi.
Ko da yake ya ki yin ƙarin bayani, Amma ya yi nuni da cewa a shirye APC take don dakile duk wani yunkurin ’yan adawa, ko da yake bai yi ƙarin bayani ba.
Ganduje ya ce, “Ba za mu bayyana shirinmu ba, amma mun riga mun shirya musu. Nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu yana ƙara karfafa jam’iyyar,” in ji shi.
Ganduje ya kuma jaddada burin APC na karɓe fiye da jihohi 21 da take mulki a halin yanzu, yana mai bayyana ƙwarin gwiwa cewa jam’iyyar za ta samu karin jihohi ta hanyar sauya sheka ko zaɓe mai zuwa.
“Wasu gwamnoni za su iya dawowa cikinmu, ko kuma mu kayar da su a zaɓe. Ko ma mene ne dai, muna faɗaɗa mulkinmu. Muna gamsu da inda muke, amma ba za mu tsaya a iya nan ba.”
Da yake tsokaci kan sauya shekar da wasu kusoshin APC suka yi a kwanan nan da kuma rikicin cikin gida na jam’iyyar, Ganduje ya tabbatar da cewa tafiyarsu ba ta da wani tasiri mai yawa.
“Manyan mutane daga wasu jam’iyyu suna dawowa APC. ’Yan ƙalilan da suka tafi kuma babu wata illa ta a-zo-a-gani da za sai yi,” in ji shi.
Dangane da sukar da ake yi kan zargin gwmanatin Tinubu da nuna bangaranci a rabon muƙamai, Ganduje ya dage cewa ana raba mukamai daidai kuma jam’iyyar na tattara bayanai don tabbatar da adalci.
Ya ce, “Muna tara alƙaluman nadin mukamai don nuna cewa babu nuna bambanci a nadin mukaman shugaban kasa,” in ji shi.
Kalaman Ganduje na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da cukumurdar siyasa gabanin babban zaben 2027, inda jam’iyyun masu mulki da na adawa ke neman karfafa kawance da kuma sake dabaru.