Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama wani dan daba kan zargin kashe wani limami saboda ya hana shi shan wiwi a kusa da masallaci.
Cikin sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Laraba, ya ce dan daban mai suna Yusuf Haruna mai shekara 18 wanda aka fi sani da Lagwatsani ya caka wa limamin wuka a bayansa yana tsaka da alwala.
- Jadon Sancho zai koma zaman aro a Dortmund
- Iran ta lashi takobin daukar fansa kan tagwayen hare-haren Kerman
An kamo Lagwantsani ne bayan ya tsere kamar yadda SP Kiyawa ya wallafa cikin sanarwar a shafinsa na Facebook.
“A ranar 31 ga watan Disambar 2023 da misalin bakwai da rabi na dare, an samu rahoto daga wani Musa Yunusa da ke unguwar Jakara kan cewa da misalin karfe bakwai na safe wani Yusuf Haruna ya caka wa Malam Sani Mohammed Shuaibu wuka a baya yana tsaka da alwala.
“Ya caka masa wukar sakamakon ya gargade shi kan ya daina zukar tabar wiwi a kusa da masallaci,” in ji sanarwar.
A cewar Kiyawa, sakamakon haka ne malamin ya samu rauni wanda aka garzaya da shi Asibitin Murtala inda likitoci suka tabbatar da ya rasu.
Kakakin ’yan sandan ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kan wannan lamari kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.