Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan dari da hamsin da ɗaya da dubu dari takwas da sittin da uku (N151,863,895.97) domin sake gina wani masallaci da wani matashi ya cinna wa wuta a yayin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba a cikin jam’i a Tiga Gadan da ke Karamar Hukumar Gezawa, a watan Mayun bara.
Aikin sabunta masallacin ya kunshi gina makarantar Islamiyya tare da ofis da bandaki da kuma rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana tare da tankin ruwa na sama.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya sanar amincewar sake gina masallacin ya biyo bayan alkawarin da Gwamna Abba Kabir ya yi a lokacin da ya ziyarci wurin da abin ya faru.
Ya yi kira ga mutanen kauyen Gadan da su saka wannan karimci ta hanyar bayar da goyon bayan da ake bukata don tabbatar da nasarar kammala aikin, da kuma samar da kariya ga sabbin gine-ginen.
- Yadda kotu ta yanke wa wanda ya kona mutane a cikin masallaci hukuncin rataya a Kano
- Amarya ta kashe uwargida da wuka a Katsina
- An yanke wa wanda ya yi wa agolarsa fyaɗe ɗaurin rai-da-rai
A ranar Litinin ne Babbar Kotun Musukunci ta yanke wa Shafi’u Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kona masallacin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 23.