✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na rungumi aikin gona — Sheikh Jingir

Ban taba samun amfanin gona da yabanya irin ta daminar bana ba.

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa (JIBWIS).

Yana da gonaki a jihohin Filato da Kaduna da Bauchi da Gombe, inda yake noma kayayyakin amfanin gona iri daban daban.

A tattaunawa da Aminiya, ya bayyana abin da ya karfafa masa gwiwar rungumar aikin noman. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Me ya karfafa maka gwiwar rungumar aikin noma, duk da matsayin da kake da shi?

Abin da ya karfafa mani gwiwar rungumar aikin noma, shi ne ni mutum ne, don haka ina ci, ina sha, ina da bukatar sanya tufafi, ina da bukakar wurin zama, ina da matan aure guda 4, ina da ’ya’ya guda 42.

Ka ga duk wadannan iyalai nawa, na san duk bukatarsu iri daya ce da tawa, kowa yana ci, yana sha. Ka ga noma ya kama mu.

Hak kuma ina gudun abin kunya, ba na son bashi, kuma na san haramcin cin dikiyar mutane.

Don haka na watsar da duk wani abu da zai kawo mani girman kai, na rungumi aikin noma.

Ina noma ni da iyalina da sauran wadanda suke bin irin tawa. Kuma muna cikin rufin asiri.

Domin da wannan noma nake samu nake ci ni da iyalina. Kuma abin da za a yi a samu lada a Lahira, babu kamar noma.

Ka ji dalilin da ya sa na rungumi aikin noma.

Kamar wadanne irin kayan amfanin gona ne kake nomawa?

Kayayyakin amfanin gonar da nake nomawa, sun hada da shinkafa da masara da wake da gero da dawa da maiwa da gurjiya da kayan marmari da kuma ’ya’yan itatuwa.

A daminar da ta gabata ka noma kamar buhu nawa?

Gaskiya a daminar da ta gabata, na samu amfanin gona mai yawa. Amma a yanzu ba zan iya ce maka ga yawan buhunhunan amfanin gonar da na noma ba.

A takaice noman da na yi a daminar da ta gabata, ya ishe ni ci tare da dukkan iyalaina.

Bayan haka, na sayar da wasu daga cikin kayan amfanin da na noma, na sayi kayan aikin noman da na yi a daminar bana.

Ka ga ai noma ta yi albarka, domin ga abincin da za a ci na shekara ga kuma wanda aka sayar aka yi noman bana.

Yaya ka ga yanayin daminar bana da yanayin amfanin gonakinka?

Gaskiya a daminar bana, na ga taimakon Ubangiji, domin ban taba samun amfanin gona da yabanya irin ta daminar bana ba. Saboda haka na gode wa Allah.

Kamar yadda na saba a kowace damina, a daminar bana ma a gonakina na noma shinkafa da masara da wake da gero da dawa da maiwa da gurjiya.

Sannan dukkansu, Allah Ya ba ni su a daminar bana. Kuma da yake ina shiga daji, na ga makwabtan gonakina su ma amfanin gonar da suka shuka ya yi kyau sosai.

Zuwa yanzu sababbin kayan amfanin gona, sun fito har sun fara cika kasuwanninmu.

Yanzu idan ka je Kasuwar Jingir da ke nan Jihar Filato da Kasuwar Saminaka da ke Jihar Kaduna, za ka ga sababbin kayan amfanin gona, kamar masara da shinkafa da doya da gwaza da gyada da dankalin Hausa da dankalin Turawa duk sun fito.

To ka ga idan da ta tawa ce, ya kamata kafofin yada labaran Nijeriya, su zagaya, su yi ta daukar wannan labari, su yada wa duniya.

Domin a ga irin baiwar ruwan da Allah Ya yi mana, Ya kare mu daga fari, ya karbi addu’o’in rokon ruwan da muka yi, Musulmanmu da Kiristoci, lokacin da aka samu wani dan tsaikon ruwa sama.

Yanzu Allah Ya karbi addu’o’inmu, an samu ruwan sama kusan a ko’ina a Nijeriya.

Don haka, ina cike da farin ciki da wannan baiwa da Allah Ya yi mana.

Kuma ina kira ga ’yan jaridar Nijeriya, su yayata ni’imomin da Allah Ya yi mana a Nijeriya.

Na san akwai abokan gabar Nijeriya, na kusa da na nesa, suna turo ’yan jaridarsu Nijeriya, su yi ta bata sunan Nijeriya.

A kullum idan za su yi labari a kan Nijeriya, sai dai su ce muna cikin kunci ko fari, babu ruwansu da labarin ni’imar da Allah Ya ba mu, don ba sa son wannan daukaka da Allah Ya yi mana.

Nan tsakanin yankin Jingir da ke Jihar Filato da yankin Saminaka da ke Jihar Kaduna, yawan mutanen da suka tafi aikin Hajji a bana da kudin noma, abin a yi wa Allah godiya ce.

Wai ina ’yan jaridarmu ne? Me ya sa muka yi shiru, Turawa suna ta yi mana barna?

Yanzu kamar a bangaren gwamnati, a sa jihohin Filato da Kaduna da Barno a wani shirin noma na gwaji.

An debi wuraren noma, za a yi noma. Har sun gayyace ni, na tura wakilaina, a wajen kaddamar da wannan shiri.

A wannan shiri, za a bai wa kowane manomi gona hekta 1. Gwamnati za ta yi shuka, ta girbe, sannan ta ware kashi 20 na amfanin gonar da aka noma, ta bai wa manomin da aka bai wa wannan gona.

Kashi 80 kuma ta raba 2, ta sayar da kashi 40, kashi 40 ta bai wa manomin ta ce ya je ya sayar ya ci gaba da noma gonarsa.

Sannan a sake debo wasu manoman, a yi masu irin wannan shiri. Ka ga ni a wurina, wannan shiri yana da kyau.

Wane sako ne kake da shi zuwa ga manoma?

To sakona ga ’yan uwana manoma shi ne Ubangiji Ya ba mu damar yin noma, don mu ci halal.

Manoma ku duba ku ga irin nasarorin da na samu a gonakina.

Babu takin gwamnati ko kwaya daya da na zuba a gonakina a daminar bana.

Tun kafin na tafi aikin Hajji, na ware komai na aikin gonakina. Na sayi takin zamani da takin kashin kaji da takin shanu da maganin feshi da zan yi amfani da su da kuma kudaden wadanda za su yi mani aikin gonakin.

Kuma ga shi Allah Ya yi wa wannan noma da na yi a bana albarka, gonakin sun yi kyau sosai. Don haka, ina kira ga jama’a mu tashi, mu yi noman nan, domin mu kare mutuncinmu.