Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru Zariya ta hori manoma da kada su yi fargaba bisa yadda Gwamnatin Tarayya ke shigo da abinci daga ƙasashen waje.
Shugaban Cibiyar, Farfesa Ado Yusuf ya ba da shawarar ce a yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron bita da tsare-tsaren aikin noma na shekarar 2025 da ya gudana a dakin taro na Tanimu Balarabe da ke Cibiyar IAR Samaru, Zaria.
- Abin da ya hana ni cika alƙawarin da na yi wa ma’aikata — Gwamnan Sakkwato
- Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a Sakkwato
Ya tunasar da manoma cewa, nau’o’in abincin da suke nomawa ba a kasar nan kadai ake amfani da su ba, don haka kayan amfanin gonarsu zai ci gaba da daraja a wasu sassa na kasashe duniya da suke neman su.
Farfesa Yusuf ya kara da cewa, har yanzu abubuwan da ake nomawa a kasar nan ba ya wadatar da bukatun ‘yan kasa ballantana a rasa yadda za a siyar da su.
Sai dai kuma shugaban cibiyar ya yi kira da a dauki matakan da suka dace wajen kayyade irin kayan abincin da ake shigowa da su don cim ma burin da ya sa gwamnati ta dauki matakin.
Masanin aikin gonar daga nan sai ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta wadata manoma da muhimman kayan aikin noma, domin ci gaba da ba su ƙwarin gwiwar aikin gona, domin kada shigowa da kayan abincin ya karya masu gwiwa.
Ya tabbatar da cewa, duk da kokarin gwamnati na shigowa da abinci daga waje, wanda ya karya farashin kayan abinci, manoma sun sami ribar noma daidai gwargwado a daminar bara.
Farfesa Yusuf ya ƙara da cewa, “ina cikin masu son ganin manoma sun sami ribar noma, amma kuma ba na son ganin an tsawwalawa wa jama’a ta inda farashin kayan abinci zai hana talaka sayen abin da zai ci.”
Shugaban Cibiyar IAR ya kara da cewa, duk da Nijeriya na shigowa da kayan abinci, har yanzu ana kuma safarar kayan gona zuwa wasu ƙasashen waje, don haka ya jaddada buƙatar da ke akwai ta samar da ingantattun kayan aikin noma kuma cikin farashi mai rahusa da manoma za su iya mallaka.
Ya bayyana cewa, hauhawar farashi da tsadar kayan noma na iya hana manoma noma isasshen abinci ga kasa, wanda haka zai iya sanadin durkushewar mafi yawa daga cikinsu kuma ya sa su watsar da aikin gona.
Don haka ya roƙi gwamnatin da ta gaggauta ɗaukar matakan sauƙaƙa wa manoma da ribanya ƙwazonsu da wadata ƙasa da abinci.
Da yake tsokaci dangane da ayyukan cibiyar, Farfesa Yusuf ya ce, a wannan shekara ta 2025, cibiyar za ta gudanar da ayyukan bincike a kan aikin noma har sama da guda 180, yayin da za ta bai wa wasu aikace-aikacen gona 32 muhimmanci don bai wa manoma ingantattun dabaru tare da sauke nauyin da ke kan cibiyar na habaka aikin noma a kasa.
Tun farko da yake nasa jawabin, shugaban taron kuma Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Kabir Bala ya ce, duk da dai yana halartar taron ne a karo na karshe a matsayinsa na shugaban jami’ar duk da haka cibiyar za ta ci gaba da samun dukkan taimako da kwarin gwiwar da take bukata daga gare shi.
Farfesa Bala wanda ya nuna jin dadinsa bisa yadda aka tattara masana aikin gona daga jihohi daban-daban na kasar nan, inda ya yi fatan za a fito da wata matsaya da za a habaka samar da abinci da kuma saukaka wa ‘yan kasa yadda za su same shi cikin sauki kuma a wadace.
Sai dai kuma ya roki gwamnati da ta samar da karin kudade ga cibiyar don ci gaba da gudanar da ayyukan binciken sababbin dabarun aikin gona.