Matatar Mai ta Dangote ta bayyana cewa Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) bai fara sayen fetur daga gare ta ba.
Sanarwar da Mamatar Dangote ta fitar ta ce kamfanin bai ma kammala kulla yarjejeniyar kasuwanci da NNPC kan tataccen man fetur dinsa ba, ballantana NNPC ya fara daukar man domin sayarwa.
Kamfanin ya ce ya yi wannan bayani ne sakamakon wasu labarai marasa tushe da ke cewa NNPC ya fara daukar man fetur daga Matatar Dangoye domin sayar da lita a kan N897.
Amma hukumar gudanarwar Matatar Dangote ta ce “ba mu kammala yarjejeniyar sayar da tataccen man ga NNPC ba, ballanana maganar farashi ta taso.”
Wannan bayanin yana kunshe ne a cikin sanarwar da kakakin Matatar Dangote, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
A ranar talata ne dai Matatar Dangote da sanar a hukumance cewa ta fara fitar da tataccen man fetur kuma da zarar sun kummala kulla yarjejeniyar da NNPC man zai shiga kasuwa.
Shugaban Rukunkin Kamfanonin Dangote, kuma mamallakin matatar, Alhaji Ali Dangote, ingancin man fetur din matatar zai yi goyagga da na kasar Amurka da manyan kasashen duniya, kuma ba shi da illa ga injina.
A cewar Dangote, aikin matatar zai rage wa Najeriya dogaro a kan Dalar Amurka da kashi 40 cikin 100.
Hukumar harkokin mai (NMDPRA) ta sanar cewa matatar za ta fara samar da lita miliyan 25 na fetur a kullum a cikin gida a Najeriya, zuwa watan Oktoba kuma za a kara yawansa zuwa lita militan 30.
A ranar talata ne dai aka kara farashin mai a Najeriya, lamarin da ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce.