A karon farko Nijeriya za ta fara fitar da tataccen man fetur zuwa nahiyyar Asia kamar yadda wata majiya daga Matatar Dangote ta sanar.
Majiyar ta ce wani jirgin ruwan dako mai ɗauke da tan 90,000 na man fetur zai yi jigilar daga Matatar Dangote da ke Nijeriya zuwa nahiyar Asia.
- HOTUNA: Yadda Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a harin Benuwe
- Hare-haren Benuwe: Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ambato majiyar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta tana cewa “yanzu jirgin ruwan Mercuria zai tafi Asia a ranar 22 ga Yuni.”
“Muna sayar da kayanmu ne ga waɗanda suka yarda su ba mu farashi mafi yawa. Mai saye na da haƙƙin kai wa duk inda yake so,” in ji kakakin matatar mai ta Dangote.
Darektan a kamfanin Horizon Engage, Clementine Wallop, ya alaƙanta fitar da man da matatar za ta yi a matsayin wani gagarumin tasiri na zama abar dogaro wajen samar da mai a faɗin duniya.
Tun bayan da matatar mai karfin tace ganga 650,000 na ɗanyen mai a kowacce rana ta fara fitar da fetur a bara, jiragen ruwan da ke ɗaukar man zuwa Yammacin Afirka ne.
Matatar man ta dala biliyan 20 da mai kuɗin Afirka Aliko Dangote ya samar a birnin Legas, ta fara aiki a watan Janairun shekarar da ta gabata.