Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa.
A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira.
- Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina
- Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi
Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.
Rahotanni sun nuna cewa farashin ya fi ƙaruwa a Arewa, yayin da Legas ke da mafi ƙarancin farashi.
Kamfanin MRS Oil & Gas na jigilar mai daga Legas zuwa sassa daban-daban na ƙasar.
Duk da haka, ba a bayyana takamaiman wajen da aka sayo sabon man fetur ba, amma yanzu ana sayar da shi a farashin da ya bambanta da na baya.