✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya

Sabbin matatun uku idan an kammala su gaba ɗaya za su iya tace ganga 140,000 na man fetur duk rana.

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA, ta bayar da lasisin kafa sabbin matatun man fetur uku a wasu jihohin ƙasar uku.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, wadda shugabanta, Farouk Ahmed ya bayyana ta nuna.

NMDPRA ta ce ta bayar da lasisin gina sabbin matatun man ne a jihohin Abia da Delta da kuma Edo.

“Za a buɗe Matatar Eghudu wadda za ta iya tace ganga 100,000 a kullum a Jihar Edo.

“Za kuma a buɗe Matatar MB wadda za ta riƙa tace ganga 30,000 a kullum a Jihar Delta, sai Matatar HIS wadda ita kuma za ta riƙa tace ganga 10,000 a kullum a Jihar Abia.”

Hukumar ta ce sabbin matatun uku idan an kammala su gaba ɗaya za su iya tace ganga 140,000 na man fetur duk rana.

Bayanai daga hukumar ta NMDPRA sun nuna cewa Nijeriya na da matatun man fetur tara, ciki har da sabuwar matatar Dangote da ke birnin Legas.

Waɗannan matatu na tace ganga 974,500 a duk rana, yayin da Matatar Dangote kaɗai ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana.