Ministan Sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi, ya sanar da cewa ya daina bai wa mata mukami a sakamakon rudanin da hakan yake haddasawa a tsakanin mata.
Da yake jawabi yayin taron kungiyar mata ‘yan kasuwa ta Najeriya (ANWBN) wanda aka gudanar a karshen makon da ya gabata, Amaechi ya ce galibin matsalolin da mata ke fuskanta su ke jefa kawunansu a ciki.
A cewarsa, da zarar an bai wa mace mukami, sai a fara tsegumin cewa ta bayar da kanta ne ba tare da ta cancanci wannan mukami ba.
Sai dai ya ce yana da kyau a rika fifita mata wajen bayar da mukami saboda sun dara maza hazaka.
“Ban yarda da yadda maza ke rinjayar mata ba wajen bayar da madafan iko, kuma ban yarda da yadda ake ware wata kujera ba musamman saboda mata, don dalilin shi ne mata sun fi maza basira nesa ba kusa,” a cewar Ministan.
“An nada Amina Muhammad a matsayin Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya saboda kwazo da kuma rawar gani da ta taka a fannoni daban daban ba don kasancewarta mace ba.”
Tsohon Gwamnan na jihar Ribas ya ce duk wata mace da ya taba bai wa mukami ta cancanta ne, sai dai gunagunin da ke biyo baya ya sanya ya dakata da bai wa mata mukami.
“Duk wata mace da na taba bai wa mukami ta cancanta, amma da zarar ka bata sai tsegumi daga ‘yan uwanta mata ya fara biyo baya cewa akwai wata alaka a tsakani da ta sanya ta samu wannan mukami.”
“Wannan shi ne dalilin da na daina bai wa mata mukami saboda duk wata matsala su ke haddasa ta a tsakaninsu.”