Wata dabi’a da aka jarrabi mutane da yawa da ita a wannan zamani, maza da mata, manya da yara, ita ce zuwa wajen matsafa, bokaye, ’yan duba da ’yan tsibbu, don neman taimako a wajensu, domin sanin abin da zai zo nan gaba ko neman biyan wata bukata, wadda wannan ba karamar halaka ba ce mai tabarwa duniya da Lahira.
Akasari mu mata mu ne muka fi afkawa cikin wannan mummunar dabi’a, musamman ’yan matan da suke fafutikar neman mazan aure ido-rufe kamar yadda bincike ya nuna ko kuma matan aure da ke da kishiyoyi ko ake shirin yi musu.
- Sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta za ta fara aiki a Sudan —MDD
- Hukumar Aikin Hajji ta lashe amanta kan karin Kudi
Wannan mummunar dabi’a ta hallakar ko in ce tana kan hallakar da kaso mai yawa na mata a wannan zamani.
Raba miji da matarsa:
Wannan dabi’a ta zama ruwan- dare a tsakanin ’yan mata da matan aure. Sai ka ga budurwa da taimakon iyayenta sun himmatu wajen kai-kawo wurin bokaye da malaman tsibbu duk don su ga ’yarsu ta auri wani saurayi da ake kwadayin abin da ke tattare da shi.
Su ma a nasu bangaren, matan da ke gidan mazansu suna kokarin ganin sun mallake mijin da suke tare da shi ko kishiyar da suke zaune da ita domin tabbatar da komai suka ba da umarni haka za a aiwatar da shi, ba tare da yi musu jayayya ba.
A wasu lokuta ma wannan ba iyaka bukatar su ba ke nan ba, har ma son ganin sun kori kishiyar da suke zaune da ita ko kuma ganin sun raba mijin da ’yan uwa da abokan arziki, kai a wasu lokuta ma ita kanta rayuwar suke kokarin tsaidawa.
Ana samun mata masu yawa da dabi’ar bin ’yan tsibbu da bokaye saboda manufofi daban-daban.
Me ke kai mata ga wannan dabi’a? Dalilan da suke kai mafi yawan mata wajen bokaye su ne kamar haka:
1. Jayayya da umarnin Allah
2. Fada da kaddarar Allah
3. Saba wa umarnin Manzon Allah (SAW)
4. Rashin imani 5.
Rashin tausayi
6. Hassada
7. Rashin tawakkali
Manyan hadduran bin bokaye
Daga cikin manyan hadduran da wannan mummunan aiki ya kunsa akwai:
1. Shirka ga Allah: Wannan dabi’a da kuma cika sharuddan da aljanun da bokayen ke aiki da su ne bakar shirka.
Domin bauta wa wanin Allah ne da neman yardarsa, wato sanya masa kishiya ta hanyar mika wani hakkin ibada zuwa ga waninSa, kamar yanka dabba domin waninSa ko cika wasu sharuddan da ba Allah ne Ya ce a cika su ba.
2. Rashin dogaro ga Allah: Mai sihiri ko mai neman a yi masa sihirin bai yarda cewa Allah ne abin dogaronsa ba, kuma Shi ne Mai taimakonsa ba, kuma Shi kadai ne Mai iya fitar da shi daga kowace matsala, Ya kuma dauke masa kowa ce irin damuwa.
3. Cutar da mutane: Wannan kuma babban abu ne da ya shafi hakkin shi wanda aka cutar, domin har abada Allah zai bi ki da alhakinsa har sai in ya yafe miki, bayan babban laifin shirkar da aka yi.
4. Yada firgici da wasi-wasi: Idan sihiri ya yadu a tsakanin al’umma, to komai kankantar abin da ya faru ga mutum ko wani nasa sai ya fara zaton cewa sihiri wani ya yi masa, tun bai yi bincike ko ya je wurin likita ya rasa magani ba. Wannan na yawan faruwa a wannan lokaci da muke ciki.
5. Janyo fushin Allah Madaukaki: Duk al’ummar da ta fada cikin wannan mummunan hali, kuma malamanta suka yi shiru ba su fadakar da mutane kan hadarinsa ba, to fushin Allah zai iya fada mata kuma ta rasa albarka, ta rasa zaman lafiya, kamar dai halin da kasarmu take a ciki yanzu.
Rubutawa: Samira Bello Shinko [email protected]