Rahotanni na cewa daliban nan mata guda biyu da wasu ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya da ke Gusau sun kubuta.
Daliban sun shaki iskar ’yanci ne bayan kwanaki 12 da yin awon gaba da su a yankin Sabon Gida da ke gundumar Magami ta Karamar Hukumar Gusau.
- Karashen Zabe: EFCC ta baza jami’anta 100 a Kano
- Gwamnati ta karrama limamin da ya tausasa kyanwa yana jan Sallah
Kungiyar Daliban Jami’ar ce ta tabbatar da sakin daliban, sai dai ba ta yi karin haske ba dangane da ko an biya wasu kudade a matsayin fansa.
Mai magana da yawun kungiyar daliban, Umar Abubakar, ya ce jami’ar ta kidime da farin ciki bayan samun labarin sakin daliban, yana mai yaba wa mahukunta jami’ar da suka yi tsayuwar daka wajen cimma wannan babbar nasara.
Aminiya ta ruwaito cewa tun bayan faruwar lamarin ne aka aike da karin jami’an tsaro zuwa yankin Sabon Gida da ke Jihar Zamfara, bayan an sace wasu dalibai ’yan mata biyu.
Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne dai suka sace ’yan matan su biyu, bayan sun balle gidan da suke haya a yankin na Sabon Gida.
Maharan dai sun balle gidan ne ta karfin tsiya, inda kua suka kulle masu gadinsa sannan suka kwace wayoyin daliban wadanda ke karatu a Sashen Nazarin Halittu na jami’ar, kafin daga bisani su yi awon gaba da su.
Sabon Gida dai nan ce unguwar da jami’ar take, kuma ba ta da nisa da mazaunin makarantar na dindindin. Galibi dai dalibai kan kama haya a can suna zama.
To sai dai bayan an kai harin, rahotanni sun ce daliban sun gudu sun bar gidajen nasu, amma daga bisani sun sake dawowa bayan an kai jami’an tsaro.