Rundunar ’yan sanda da ke Jihar Kogi ta tabbatar da cewa dalibai 24 da aka sace a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence da ke Osara a Karamar Hukumar Adavi.
Williams Aya, kakakin ya bayyana wa manema labarai a ranar Litinin cewa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne dai ’yan bindigar suka kai hari makarantar, suka sace daliban da ke karatu domin jarrabawarsu da ke tafe.
An ce, ’yan bindigar sun shiga wani dakin karatu ne a cikin makarantar suka bude wuta a sama suka firgita daliban.
Amma rundunar ta ce kawo yanzu an iya kubutar da 14 daga cikin wadanda aka sace.
Williams Aya ya ce wata daliba da ta kubuta ta ce lokacin da aka shiga dakin karatun su 24 a ciki.
Sai dai wasu daga cikinsu sun samu damar tserewa yayin da jami’an tsaro suke bata kashi da ’yan bindigar.
Ya kara da cewa, an yi nasarar kubutar da 14 daga cikin daliban a wani daji dake Obajana a Karamar Hukumar Lokoja.
Ya ce rundunar hadin gwiwar sojoji da ’yan sanda da DSS da ’yan Banga ne suka yi nasarar ceto daliban.
Ya ce wutar da ’yan bindigar suka gani daga rundunar hadin gwiwar ta razana su suka firgice suka gudu da sauran daliban.
“A yanzu haka, rundunar na cikin daji suna laluben inda aka boye daliban domin kubutar da su da kuma tabbatar da cewa an hukunta duk wani mai hanu a ciki.”