✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wike zai rushe shaguna 500 cikin awa 24 a Abuja

FCDA ta ba wa masu shaguna a kan titin Karmo zuwa Dei-Dei awa 24 su kwashe kayansu za ta yi rusau

Hukumar Kula da Cigaban Abuja ta bai wa wadansu masu shaguna a gefen titi har guda 500 wa’adin awa 24 su tashi domin rushe su.

Shagunan da za a rushe suna kan kan hayar Karmo zuwa Dei-Dei ne da ke karkashin kulawar hukumar.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Garba Jibril, jami’in hukumar da yankin ke karkashin kulawarsa yana cewa, an sha yi wa masu gina irin wadannan shagunan gargadi amma ba su yarda ba.

Ya ce, an fada musu cewa za a rusa shagunan da suka gina ba bisa ka’ida ba, ba wannan ne karo na farko ba.

Garba ya ce, babban daraktan hukumar, Mukhtar Galadima, ya yi zama da wadanda abin ya shafa inda ya fahimtar da su muhimmancin rushe gine-ginen, saboda barazana da suke yi ga harkokin tsafta da tsaron yankin.

Ya ce, wadannan shagunan sun taka dokar tsarin birnin da aka yi aka ajiye tun da dadewa domin samun cigaba mai dorewa.

Garba Jibril ya ce an umurci masu shagunan su koma Kasuwar Karmo da gwamnati ta samar, amma sun ki komawa.

Jami’in da yankin da za a rusa ke karkashin kulawarsa ya ce an bayar da aikin gyaran hanyar unguwar Life Camp zuwa Dei-dei, amma zaman shagunan a kan hanyar ya kawo wa masu aikin hanyar tsaiko wurin shiga da kayan aiki domin farawa.

Ya ce, wannan wa’adi na awa 24 ba abin wasa ba ne; Duk wadanda suka tsaya jan jiki ba su debe kayansu ba za su ga abin da ransu bai so ba.