✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina mata su rika samun mukaman gwamnati —Fatima Jajere

Jajere ta sha alwashin shige wa matan Arewa Maso Gabas gaba a harkar siyasa.

Hajiya Fatima Isa Jajere da ke neman kujerar Shugabar Matan Jam’iyyar APC ta shiyyar Arewa Maso Gabas a zaben da jam’iyyar za ta gudanar, ta ce burinta shi ne ta ga ana damawa da mata a harkokin gwamnati.

Jajere, ta ce tana da burin ganin mata sun samu akalla kaso 35 cikin 100 na mukaman gwamnati a dukkan matakai.

Da ta ke zantawa ta da wakilinmu kan manufofinta na tsayawa takarar kujerar, ta ce don ta ceto matan yankin ne ta kuma ga ana damawa da su a siyasa.

A cewarta mata na bayar da kuri’u sosai a lokutan zabe amma har yanzu ba a ba su mukamai sosai a siyasance, shi ya sa fitowarta za ta kara musu himma su gane cewa za su samu wakilci idan ta zama shugabarsu.

Jajere ta yi wa mata albishir da cewa za ta kara sama musu hanyoyin koyon sana’o’i a bangarori daban-daban daga gwamnati da ma kungiyoyi masu zaman kansu, karkashin gidauniyarta ta ‘F-Jajere Foundation’.

Ta kara da cewa tana da burin ganin mata sun samu ci gaba a tafiyar da ake yi yanzu ba kamar yadda aka bar su a baya ba.

Tun da farko ta ce yanzu duk inda ta ji wani abu na mata sai inda karfinta ya kare wajen nemo musu don su amfana.

Kazalika, ta yi kira ga shugabanin siyasa da cewa su dinga jan mata a jika ana yin abubuwa da su domin kara musu kwarin gwiwa su bayar da hadin kai da goyon baya a yi nasara a zabe idan lokaci ya yi.

Ta ce matan yankin mutane ne da kunya ba ta barin su su yi siyasa saboda addini da kuma al’ada, wanda a wasu lokuta idan mace ta fito siyasa sai a rika yi mata wani irin kallon ko bata mata suna, hakan ne ya taimaka wajen barin su a baya ba kamar takwarorinsu na Kudancin kasar nan ba.

Daga nan, ta yi kira na musamman ga mazaje da su dinga barin matansu suna fitowa ana damawa da su a siyasa suna ci gaba da yar tasu gudummawa kuma a daina yi musu mummunar fassara.