Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a ranar Talata 16 ga watan Janairu, 2024, zai ziyarci Abuja babban birnin kasar domin kaddamar da wasu littafai guda biyar da tsohon mashawarcinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya wallafa.
Buhari wanda tun bayan sauka daga kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023 bai sake waiwayar babban birnin kasar ba, zai halarci bikin kaddamar da littafan ne tare da Shugaban Kasa Bola Tinubu wanda zai kasance babban bako na musamman.
- ISWAP ta datse wa masunta biyu hannu a Borno
- Kotu ta ba da belin tsohon Ministan Lantarki Olu Agunloye
Haka kuma, ana sa ran tsohon Shugaban Najeriya wanda zai zama uban taron, Yakubu Gowon zai halarci bikin tare da Janar I.B.M Haruna mai ritaya, da sauran manyan baki.
Akwai kuma tawaga ta musamman daga masarautar Saudiyya da za ta halarci bikin karkashin jagorancin Yarima Abdulaziz bin Faisal Al Saud, yayin da attajirin dan kasuwar nan, Mohammed Indimi, zai kasance babban mai kaddamar da littafan.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Alhamis a Abuja dangane da bikin, Femi Adesina ya ce akalla marubuta 100 ne suka bayar da gudunmuwar wallafa litattafan ciki har da masu adawa da tsohon shugaban kasar.
A cewarsa, litattafan za su yi bayani karara kan dalilan da suka sanya Buhari ya ɗauki wasu matakai a lokacin da ya riƙe da madafun iko sabanin yadda ake hasashe da yada jita iri-iri.
Aminiya ta ruwaito cewa, littafin wanda aka wallafa cikin mujalladai biyar mai taken; Muhammadu Buhari: The Nigerian Legacy 2015-2023, Dokta Udu Yakubu ne ya yi bitarsa.
Da yake jawabi, Dokta Yakubu ya ce babban makasudin wallafa littafin mai mujalladi biyar shi ne bayar da cikakken labari a kan gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Ya shaida wa manema labaran cewa, an fara rubuta littafin ne a farkon shekarar 2022, amma sai daf da lokacin da shekarar ta fara bakwana aka nemi gudunmawar wasu marubutan.
A cewarsa, an zabo masu bayar da gudummuwar ce daga bangarorin ilimi, kafafen yada labarai, cibiyoyin bincike da kuma masana masu zaman kansu.
Ya bayyana cewa, littattafan sun samu tabarrakin marubuta da dama, editoci, masu bita da nazari ciki har da gogaggen editan nan Ambasada Dokta Chijioke Wigwe da dai sauransu.
“Wannan lamari ba aiki ba ne da muka yi shi cikin sauƙi, amma ina farin ciki da muka kammala har muka kai karshensa duk da irin kalubalen da muka riƙa fuskanta,” in ji Dokta Yakubu.