✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta datse wa masunta biyu hannu a Borno

Mayakan na ISWAP sun fusata ne bayan an gano cewar masunta ba sa biyan haraji.

Mayakan kungiyar ta’adda ta ISWAP sun datse wa wasu masunta biyu hannu wadanda aka yi zargi da satar kifi a garin Marte na Jihar Borno.

Bayanai sun ce masuntan da lamarin ya shafa sun kasance masu aikin kamun kifi ne a karkashin wata babbar kungiya da ke yi wa ISWAP hidima tana kuma karbar haraji a wurinsu.

Majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin, sun shaida wa wakilinmu cewa, mayakan na ISWAP sun fusata ne bayan an gano cewar masunta ba sa biyan haraji, lamarin da ya sanya aka dauki mataki a kansu.

Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa, daga farko matakin da mayakan suka dauka a kan masuntan shi ne kwace kwalayen kifi takwas daga hannunsu.

Sai dai kuma a kokarin da mayakan suka yi na lodin kifin a kwala-kwalensu, dole ta sanya suka watsar da kwalaye biyu saboda gudun daukar nauyin da zai wuce ka’ida.

Ganin hakan ce dai ta sanya masuntan suka sake kwaso wadannan kwalaye guda biyu da aka yi watsi da su a boye, inda mayakan na ISWAP suka ayyana laifin sata kan wannan yunkuri da masuntan suka yi.

Bayan kama su ne kwamandan mayakan ya ba da umarnin a datse hannayen masunta saboda a cewarsa hakan shi ne tanadin da shari’a ta yi.