✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lakume shaguna bakwai a Adamawa

Shaidun gani da ido sun yi hasashen cewa gobarar ta tashi ne saboda yadda aka rika wasa da wutar lantarki.

Wata gobara da ta tashi a wata babbar cibiyar kasuwanci ta kone shaguna 7 da safiyar ranar Laraba a Karamar Hukumar Numan ta Jihar Adamawa.

Duk da cewa ba a gano musabbabin faruwar lamarin ba, shaidun gani da ido sun yi hasashen cewa ta yiwu gobarar ta tashi ne sakamakon yadda aka rika kawowa da dauke wutar lantarki.

Gobarar wadda ta kasance ibtila’i mai girman gaske, ta yi sanadiyar asarar dukiya ta miliyoyin nairori, lamarin da ya jefa masu shagunan cikin tarababbi gami da ban tausayi.

Mataimakin Gwamnan Jihar Adamawa, Kaletapwa Farauta wanda ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ya bayyana matukar kaduwarsa dangane da faruwar lamarin, inda a madadin gwamnatin jihar ya jajanta wa wadanda abin ya shafa da daukacin al’ummar Numan.

Da yake zantawa da manema labarai, Farauta ya bayyana lamarin a matsayin ibtila’i ga al’umma, yana mai tabbatar wa cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen bayar da tallafi ga masu shagunan da abin ya shafa

A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Numan, Christopher Sofore, ya roki gwamnati da ta kawo dauki ga masu shaguna da suka rasa dukiyarsu a dalilin gobarar.

Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa da suka zanta da Aminiya, sun yi kira ga gwamnati da ta taimaka musu wajen farfado da hanyarsu ta neman abinci.