Shugaba Muhammadu Buhari ya janjanta wa Gwamnatin Jihar Kano da kuma iyalan Wali na Jihar dangane da rasuwar tsohon Ministan Noma, Alhaji Alfa Wali.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaban Kasar ya yi alhini bisa rasuwar Alhaji Wali wanda ya misalta a matsayin babban mutum kuma abun alfahari ga Jihar Kano da kasa baki daya.
- Likitoci uku sun rasa rayukansu a Kano — NMA
- Za a kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a Saudiyya
- Buhari zai sake gina Kasuwar Sakkwato da ta yi gobara
Shugaba Buhari ya ce babu shakka za a yi kewar mamacin musamman a tsakanin al’ummar cibiyarsa da kuma Najeriya baki daya.
Ya yi addu’ar Allah Ya Jikansa da Rahama kuma ya albarkaci bayansa.
Marigayi Alhaji Alfa ya yi wa Najeriya hidima yayin rayuwarsa inda ya rike mukamin Babban Sakatare a Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da dama ciki har da ta Tsaro.
A safiyar ranar Litinin ne Allah ya yi wa Alhaji Alfa rasuwa bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar rashin lafiya inda ya yi jinya a wani Asibiti a birnin Abuja.
Tsohon Ministan Noman wanda ya rasu yana da shekaru 87 ya tafi ya bar ’ya’ya tara da suka hada da namiji daya da mata takwas.