Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana jin daɗin yadda shugaban ƙasar Bola Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa.
Buhari ya ce har yanzu Tinubu bai sauya ba daga tsari da manufofin da jam’iyyar APC ta kafa wanda har ya sanya shi kansa ’yan Nijeriya suka zaɓe shi a 2015.
- An ga watan Sallah a Saudiyya
- Dalilin da Aminu Bayero ba zai iya jagorantar hawan Sallah ba — Kurawa
Buhari ya bayyana hakan a saƙonsa na taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, wanda ya cika shekaru 73 a doron ƙasa.
Sanarwar da mai magana da yawun Buhari, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ta ce tsohon shugaban yana alfahari da alaƙarsa da shugaban ƙasar na yanzu.
Sanarwar ta ce Buhari da Tinubu sun gana ta wayar tarho a ranar Juma’a, inda a ciki Buhari ya yi Tinubu addu’ar tsawon rai da ingantacciyar lafiya da, sannan ya yi masa fatan samun nasarar a mulkinsa.
“Idan muka yi wa shugabanninmu addu’a, muna yi wa kanmu ne. Ƙasarmu na buƙatar addu’o’inmu,” in ji Buhari a ganawarsa da Tinubu.
Buhari ya ce shi da iyalansa suna godiya ga Tinubu da sauran jagororin jam’iyyar bisa ƙoƙarin da suka yi wajen kafa jam’iyyar APC, inda har ya samu nasarar zama shugaban ƙasa har sau biyu, bayan ya sha gwadawa a baya ba tare da samun nasara ba.
“Lokacin da ’yan Nijeriya suka zaɓi APC a 2023, zaɓi suka yi domin kafa tubalin sabuwar Nijeriya inda talakawa za su samu damarmakin da suke buƙata, kuma ina jin daɗi har yanzu ba a kauce daga tsarin ba.”