✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP

"Bayan tsawon watanni na tuntuɓar juna, ni Obinna Simon da aka fi sani da MC Tagwaye, na yanke shawarar ficewa daga Jam'iyyar APC na koma…

Fitaccen mai barkwancin nan wanda yake kwaiwayon maganganun tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, Obinna Simon wanda aka fi sani da ‘MC Tagwaye’ wanda yake mai nishaɗantarwa, ɗan kasuwa, kuma ɗan siyasa ya sauya sheƙa daga Jam’iyyar APC zuwa SDP.

Ya sanar da hakan ne a cikin wani saƙon da ya wallafa a dandalin sada zumunta na zamani a ranar Juma’a, ya danganta sauya jam’iyyar ne bayan tuntuɓa da yin shawarwari.

“Bayan tsawon watanni na tuntuɓar juna, ni Obinna Simon da aka fi sani da MC Tagwaye, na yanke shawarar ficewa daga Jam’iyyar APC na koma SDP.”

“Wannan gagarumin mataki ya samo asali ne daga zurfafa tunani na cewa Jam’iyyar APC ta kauce daga aƙidarta na asali kuma ta daina sadaukar da kai ga jin daɗi da ci gaban al’ummar Nijeriya. Rashin tsarin da jam’iyyar ta yi na ba da lada ga membobinta masu aminci, tsarin shugabancinta da manufofinta da ke ci gaba da haddasa wahalhalu ga masu ƙaramin ƙarfi, suna cikin dalilai na sauya sheƙar.

“Duk da haka, dimokuraɗiyyar cikin gida ta APC ta taɓarɓare sosai, inda wasu ’yan ƙalilai masu madafun iko ke tafiyar da alƙiblar jam’iyyar tare da yin watsi da muryar mafi mafiya rinjaye.

“Saɓanin haka, Jam’iyyar SDP ta fito a matsayin ginshiƙin fata nagari, tare da sadaukar da kai ga matasa, dimokuraɗiyyar cikin gida, tabbatar da gaskiya da riƙon amana. Burin jam’iyyar ne na sabuwar Nijeriya, inda jin daɗin jama’a da ci gaban dukkan ‘yan ƙasa ke da muhimmanci sosai.