Shugabannin Arewacin Najeriya sun nemi a hukunta tsohon Mataimakin Gwaman Babban Bankin Najeriya (CBN) Obadiah Mailafiya kan zargin da ya janye na cewa wani gwamnan yankin ne shugaban Boko Haram.
Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta bukaci doka ta yi aiki a kan Mailafiya, wanda a lokacin da yake zargin ya hakikance cewa gaskiya yake faɗa har da takamar cewa digirinsa na uku a Jami’ar Oxford ya yi.
Sai dai bayan kwanaki ya fito yana bayar da hakuri da cewa maganganun da ya yi a zargin ya ji su ne a kasuwar kauye.
A hirar da aka yi da shi a gidan radiyo Nigeria Info wadda ta tayar da kura, Mailafiya ya ce Boko Haram da ‘yan bindiga sun hada baki suna shirin tayar da yakin basasa a 2022 a Najeriya.
Ya ce jiragensu na ta zirga-zirgar raba makamai da kudade da kayan aiki tamkar babu dokar kulle.
Bayan hukumar tsaro ta DSS ta yi masa tambayoyi kan zarge-zargen, Mailafiya a hira da sashen Hausa na BBC ya yi da shi daga baya ya ce ya ji bayanan ne a bakin wasu Fulani a kasuwar kauye.
Sakataren Yaɗa Labaran ACF, Emmanuel Yewa ya ce zargin na da razanarwa domin yana maganar “yakin basasa da jiragen jigilar makamai da kudade ne.
“Zargi irin wannan daga mutum kamrsa babban abu ne da ya kamata a dauka da muhimmanci. Amma mun jira mu ga doka ta yi aikinta.
ACF ta bukaci manyan mutane su rika zurfafa tunani kafin su furta kalamai don kar su tayar da fitina.
– A yi cikakken bincike, inji gwamnoni
Kungiyar Gwamnonin Arewa (NFG), ta ce tana kan bakarta na a yi cikakken bincike a kan zarge-zargen.
Darekta yada labarai na shugaban kungiyar Makut Simon Macham ya ce har yanzu gwamnonin na kan matsayinsu na farko.
Sanarwar da shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalung na Jihar Filato ya fitar da farko ta nuna damuwa da zargin, wanda ta ce dole a yi bincike.
“A matsayinmu na gwamnonin Arewa mun sha yin taro a kan matsalolin tsaron yankin da ma kasa baki daya.
“A tarukan mukan yin tir da ta’addanci kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka.
“Mun kuma sha zama da Shugaban Kasa da dukkanin shugabannin hukumomin tsaro domin lalubo bakin zaren.
“Zargin daya daga cikinmu da zama shugaban Boko Haram babbar magana ce da bai kamata a yi wasa da ita ba. Muna kira da a yi cikakken bincike nan take”, inji sanarwar.
– Bayan fitowar Mailafiya daga DSS
Bayan fitowa daga ofishin DSS a Jihar Filato, lauyan Mailafiya, Yakubu Bawa, ya ce hukumar ba ta ce su sake komawa domin a ci gaba da bincike ba.
Sai dai kuma DSS din ta bayyana damuwa game da halayyar da Mailfaiyan ya nuna bayan fitowarsa, alhali ya ‘dukufa’ yana ta bayar da hakuri kan abun da ya aikata a lokacin da ya je ofishinta.
Ta bayyana damuwa cewa bayan fitowarsa kuma ya rika cewa yana nan ‘a kan kalaman da ya yi marasa dalilai’.
– DSS ta yi manyan mutane da kungiyoyi gargadi
Hukumar tsaron ta ce ba za ta yi wata-wata ba wajen yin dirar mikiya a kan duk wani babban mutum ko kungiya mai neman tayar da hankula.
Kakakin hukumar, Peter Afunanya ya ce, kamar yadda doka ta dora wa DSS alhakin ganowa da kuma dakile barazana da manyan laifuka, za ta sa kafar wando da masu neman tayar da rikici.
“Hukumar na jaddada gargadinta cewa daga yanzu ba za ta lamunci duk wani rashin da’a daga wani mutum ko kungiya da ya kamata su san daidaiba.
“Ba za mu tsaya kallon wasu marasa kishi da masu wasu manufofi su dauki doka a hannunsu ba wajen tayar da zaune tsaye.
“DSS ba za ta yi jinkiri ba wajen yin amfani da dokokin kasa ta yi maganin duk wata kungiya ko wani mutum duk matsayinsa muddin yana neman yi mata tagagi”, inji shi.
– Mailafiya ya yi shirme, inji DSS
Ta misalta kalaman Mailafiya a matsayin biye wa mutanensa na tayar da fitina, da tabbacin mutanensa na niyyar daukar doka a hannunsu.
Ya ce, a matsayinsa na tsohon darekta a Cibiyar Koyon dabarun Mulki ta Kasa (NIPSS) da ke Kuru, yana da hanyar gabatar da korafinsa ga gwamnati.
Amma abun takaici sai ya zabi bin hanyar da bai kamata babban mutum kamarsa ya bi ba.
Ya koka cewa Mailafiya bai yi amfani da damarsa ba ya sanar da jami’an tsaro ko wata hukumar tsaro bayanan da ya ce ya ji ba.
“Ya kamata a ce ya san tsarein kare bayan gwamnati da sirrinta. Amma ya zabi ya ya bi hanyar da ba ta dace da mai mutunci da matsayi irin nasa ba.
“Abun kunya ne cewa ya bai yi amfani da damar ba ya sanar da hukumomin tsaro bayanan da ya ji ba.
“Ya yarda cewa ya yi kuskure da bai yi hakan ba, wanda kuma ya nuna ya yi shirme a yadda ya yi kokarin amfani da labarun karya wajen tayar da hankula”, inji Afunanya.
“Babban abun kunyan shi ne Mailafiya wanda ya yi bayar da hakuri a lokacin da aka gayyace shi ofishinnu na Jihar Filato, daga baya ya je yana cewa yana kan maganganun da ya yi da farko.
“DSS na gargadin duk mai niyyar fakewa da sunan wayar da kan jama’a ko gangamin neman cimma wata manufa da ya yi yunkurin tayar da hankula cewa su daina.
Tun da farko hukumar ta ce ta bankado yadda wasu marasa kishi ke neman yin amfani da wasu matsaloli a sassan kasar nan wajen haddasa fitina.
“Hukumar na aiki da sauran hukumomin tsaro wajen dakile ayyukan marasa kishin”, kuma ba za ta lamunci duk yunkurin kawo rikici ba.
– Na gaya musu abun da na sani –Mailafia
Da wakilinmu ya tuntube shi ta waya, Mailafiya ya ce ya gaya da DSS abun da ya sani kuma ba shi da maganar da zai kara.
“Ba na son sa-in-sa da ‘yan DSS. Ni na riga na gaya musu iya bun da na sani kuma ba ni da abun da zan kara”, inji amsarsa ga wakilinmu.