✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram da ’yan bindiga na kara kai hare-hare –CNG

Duk da ikirarin sojoji na dakile su, mahara na ci gaba da addabar yankin Arewa

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) ta sake kokawa da cewa har yanzu kungiyar Boko Haram da ’yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankun Arewa ta Gabas da Arewa ta Yamma.

Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman ya yi kira ga Gwamantin Tarayya da ta yi hobbasa wajen kamowa da kuma hukunta ’yan ta’addan da ke ta hallaka rayuka da dukiyoyi a yankunan da kuma masu taimaka musu.

“Duk da ikirarin da gwamnati ta sha yi cewa sojoji sun gurgunta masu tayar da kayar baya a Arewa maso Gabas, kungiyar ta ci gaba nuna cewa har yanzu tana da karfin kai hare-hare da kwace sansanonin soji da kayan yaki da kuma yi wa al’ummomi fashi.

“Yayin da aka samu sauki a Jihar Zamfara a shekara daya da ta wuce, akwai damuwa ganin yadda abubuwan da ke faruwa yanzu ke barazana ga nasarorin; zaman lafiya na raguwa baya ga kuma mummunan tasirin hakan ga al’ummomi da daidaikum mutane”, inji shi.

CNG ta nuna takaici yadda ta ce wasu masu madafun iko ke kawo cikas ga sauraron shari’ar wadanda ake zargi da ayyukan ’yan bindiga da masu taimaka musu.

Sanarwar da Suleiman ya fitar mai taken ‘Za mu yaki masu kare ’yan bindiga da mukarrabansu daga shari’a’, ya bukaci a cire duk wani nau’in son rai a yaki da matsalar tsaro da yankin Arewacin Najeriya ke fuskanta.

Ya kuma zargi ’yan bindiga da neman kawo matsala a zabukan cike gurbi masu karatowa a wasu yankunan Arewa, yana mai cewa hakan ma nakasu ne ga kokarin wanzuwar tsaro a yankin.