Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce miyagu sun harbe jami’in Kwastam tare da raunata wani a Karamar Hukumar Ringim ta jihar a yayin da suke sintiri.
Kakakin Rundunar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin.
- Buhari ya ba da lamunin kashe $3.1bn domin bunkasa hukumar kwastam
- Kwastam sun kama Dala miliyan 8 a filin jirgin saman Legas
- Yadda Kwastam ta kame sama da Naira biliyan 2 a tashar jirgin saman Legas
- An gwabza fada tsakanin jami’an Kwastam da ‘yan kasuwa
“A ranar 25 ga watan Oktoba 2020 mun samu rahoton wasu bata-gari sun harbe wani jami’in Kwastam tare da raunata abokin aikinsa, yayin da suke sintiri a kauyen Kyarama.
“Sannan ana zargin cewa bata-garin sun yi awon gaba da makaman jami’an kwastam din”, inji Jinjiri.
Ya sanar da cewa rundunar ’yan sanda a jihar na ci gaba da fadada bincike domin gano wadasnda suka aikata laifin.