Gungun wasu barayi sun fatattaki masu gadin wasu manyan gonakin shinkafa, suka girbe ta suka yi awon gaba ita a jihar Taraba.
A cikin dare ne barayin suka shiga yankin Shimo da ake karamar hukumar Lau ta jihar, suka kori masu gadin suka girbe shinkafar suka tafi da ita.
Daya daga cikin masu gonakin, Abubakar Adamu, ya ce mai gadin da ya dauka aiki ya shaida masa cewa barayin sun zo ne da yawa dauke da muggan makamai. Abin da ya janyo dole suka ranta a ta kare domin tsira da rayukansu.
Ya ce, barayin sun iso gonakin ne da misalin karfe 12:30 na dare suka fara yankar shinkafar har zuwa asuba.
- Kananan Yara ’Yan Yahoo Na Yaudarar Hukumomi Don Bude Asusun Banki –EFCC
- Hotuna: Yadda zanga-zangar karin kudin lantarki ta gudana
Abubakar ya bayyana cewa yana fatan girbar buhunan shinkafa sama da 25 amma bayan satar iya buhu takwas kacal ya girba.
“Mai gadina ya shaida min cewa barayin sun fito ne daga kauyukan da ke makwabtaka da gonata, wasunsu kuma leburorin da ke aiki a gonakin namu ne.”
Malam Ibrahim Saidu wanda shi ma aka shiga gonarsa, ya shaida mana cewa, wannan babbar sata ce da aka shirya.
Domin a cewarsa, barayin da kafa suka zo wasu kuma a kan babura.
Ibrahim, wanda ya zargi mazauna kauyukan da ke kewaye da gonakinsu ne da yin satar, ya ce ya yi asarar buhunan shinkafa sama da talatin.
A cewarsa, a halin yanzu da shinkafa ke tsada, asarar da ya yi za ta kai kimanin Naira miliyan daya da dubu dari uku.
“Ba mu kama kowa ba, amma a fayyace yake cewa wadanda suka aikata wannan aika-aika ’yan yankin ne kuma wannan wani sako ne mai tsoratawa, musamman ganin yadda yawancin wadanda ke noma a yankin sun fito ne daga wajen jihar Taraba.
Bincike ya nuna cewa an dade ana satar amfanin gona a yankin noman rani na Shimo a jihar Tarba, abin da yasa yankin ya zamo abin tsoro.
Duk kokarinmu na jin ta bakin kwamishinan ’yan sandan jihar Taraba David lloyanomon kan abin da suke shirin yi abin ya ci tura.