✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kananan Yara ’Yan Yahoo Na Yaudarar Hukumomi Don Bude Asusun Banki –EFCC

Kananan yara da ke shiga harkar Yahoo Boys suna yaudarar jami'an kotu su ba su takardun mallakar asusun banki da lasisin tuki, in ji EFCC

Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta ce ƙananan yara na zuwa kotu suna yin sabuwar takardar haihuwa domin su samu damar bude asusun banki da niyyar shiga harkokin damfara ta intanet (Yahoo boys).

EFFC ta ce yaran suna kuma amfani da takarudn karin shekarun da suka samu wajen bude asusun banki da mallakar lasisin tuki daga hukumomin da abin ya rataya a wuyansu ne domin su ci moriyar abin da suka samu ta kazamar harkar zamba da yaudara.

Daraktan Hukumar EFCC na shiyyar Edo, Delta, da Ondo, Effa Okim, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da kungiyar ’yan jarida ta kasa (NUJ) reshen jihar Edo ta kai masa.

Okim ya bayyana damuwarsa kan yadda yara kananan ’yan Yahoo ke yaudarar hukumomi har su kara shekarunsu zuwa 18 domin bude asusun banki da kuma tsara ayyukansu na masha’a.

Daraktan ya ce idan aka kama wadannan yara, iyayensu na zuwa suna cewa ba su kai shekaru 18 ba, duk kuwa da cewa suna da hannu wurin aikata laifuka.

“Yahoo boys da ba su kai shekaru 18 ba, suna zuwa suna yi wa hukumomi karya cewa sun kai domin kawai a ba su damar bude asusun banki da samun lasisin tuki.

“Sai sun yi abin da ya fi karfinsu an kama su sai iyayensu su rika zuwa suna roko cewa yaran ba su kai sharkara 18 ba.

“To ina tabbatar muku, duk wanda muka kama dansa ya zo yana cewa yaron bai kai ba, to shi za mu kama”.

Daraktan Hukumar ya yi kira ga iyaye da su rika sa ido akan harkokin ’ya’yansu domin samun zuri’a na gari.