Wani ba’amurke ya yi wa karamin yaro Musulmi dan shekara shida kisan gilla a kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa.
An cafke Ba’amurken wanda iyayen yaron, wadanda Falasdinawa ne suke haya a gidansa, bayan da ya soka wa yaron wuka sau 26, ya kuma yi wa mahaifiyar munanan raunuka.
- Yadda Ba Da Dala Ga Masu Shigo Da Shinkafa Zai Shafi Farashin Ta Gida
- ’Yan Bindiga Sun Karbe Wuraren Hakar Ma’adanai A Zamfara
’Yan sanda sun sanar cewa mutumin mai suna Mista Joseph Czuba mai shekaru 71 ya kai wa Falasdinawan hari a ne gidansu da ke yankin Chicago, inda suka ba hamata iska da mahaifiyar yaron, duk da raunukna da ya yi mata, ta yi wa ’yan musu kiran neman dauki.
Suun bayyana cewa sun “gano matar da dan nata ne a uwar dakinsu, an caccaka musu wuka musamman a kirji, da sauran sassan jikinsu.”
Daga bisani kuma likitoci sun kuma ciro wata wukar soji da mutumin ne ya luma wa yaron a mara.
Yadda aka kama mutumin
’Yan sanda sun yi nasarar cafke Mista Czuba a kusa da gidan da raunaka a fuskarsa, inda suka tsare shi kan zargin kisan dan Adam, yunkurin kisa da kuma manyan laifuka na nuna tsangwama.
Shugaban Majalisar Musulmi ta Amurka (CAIR) da ke Chicago, Ahmed Rehab ya ce mahaiyar yaron ta tura wa mahaifin rubutaccen sako daga gadon asibiti cewa mutumin “ya kwankwsa kofar gidan ya yi kokarin makure matar, yana cewa , ‘Dole ku Musulmi ku Mutu.”
CAIR ta bayyana kisan a matsayin babban abin tashin hankali, a yayin da shugaban Amurka, Joe Biden ya la’anci harin, da cewa ya saba da abin da aka san Amurkawa da shi, na mutunta ’yancin dan Adam.
Ya kuma yi addu’ar samun sauki ga mahaifiyar yaron, waddda ’yan sanda ke fata za ta tsallake rijiya da baya a asibiti.
A ranar Lahadi Isra’ila ta kaddamar da luguden wuta a yankin Falasdinawa da sunan yaki da kungiyar Hamas, wadda mayakanta suka kai kutsa Isra’ila a ranar Asabarin, inda suka kashe mutum 1,400, suka sace wasu.
Hare-haren Isra’ila a yankin Falasdinawa ya yi ajalin mutane sama da 2,600 ciki har da mata da kananan yar da tsofi, yawancinsu Falasdinawa.
Kasashe masu goyon bayan Falasdinawa da Isra’ila da ke wa danniya sun la’ance ta, musamman yadda ta katse ruwan sha da wutar lantarki da man fetur d kuma jigilar abinci da kuma shige da fice a yankin Falasdina.