Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa akwai wasu masu hannu a badaƙalar almundahanar kuɗi da ake zargin ministar jin ƙai, Betta Edu ta aikata.
Atiku wanda ya yi takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jamiyyar adawa ta PDP a Zaben 2023, ya bayyana hakan yayin da yake yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan matakin da ya dauka na dakatar da ministar jin ƙan, duk da a cewarsa hakan ma kaɗai bai wadatar ba.
- Tinubu ya zaftare kasafin kudin tafiye-tafiyensa
- Dalilin da jihohi za su koma kayyade farashin kujerar Hajji — NAHCON
A Litinin din da ta gabata ce Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar, inda kuma ya umarci hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta gudanar da bincike a kanta.
Matakin na zuwa ne bayan ya fuskanci kiraye-kirayen ɗaukar mataki a kanta saboda zarge-zargen tafka almundahana, wanda ministar ta musanta.
Ministar da aka dakatar ta dai fuskanci gagarumar suka ne bayan kwarmata wasu takardun kashe kuɗi daga ma’aikatarta, waɗanda suka nuna ta bayar da umarni ga babbar akanta ta biya naira miliyan 585 cikin wani asusun ajiyar wata, lamarin da ake zargin ya saɓa ƙa’idojin kashe kuɗi na gwamnati.
A cikin wata wasiƙar martani da wani mataimakinsa na musamman Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce abin takaici ne ganin yadda shirin da aka kafa da zummar tsamo ’yan Najeriya miliyan 100 daga matsanancin talauci amma kamar yadda ake zargi ya zama saniyar tatsa ga gwamnatocin jam’iyyar APC.
Ya ce, “Ko da yake Tinubu ya cancanci yabo saboda dakatar da Betta Edu, amma muna da yakinin cewa an ɗauki matakin a makare.
“Da farko, ba shi [Tinubu] da wani dalilin wajen naɗa ta a matsayin minista a irin wannan muhimmiyar ma’aikata. Sai dai Tinubu ya fifita siyasa a kan ƙwarewa, lamarin da ya janyo wannan abin kunya.
“Wace gogewa ce Betta ke da ita a fannin ci gaba? Yaya aka yi a fifita ta a madadin Imaan Ibrahim, duk da tarin gogewarta?
“Akwai ayar tambaya yadda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya tsaya wa Betta Edu a lokacin da Majalisar Dattawa ke tantance ta”
Atiku wanda ya yi kira a yi wa ma’aikatar garambawul, yana kuma mai zargin cewa ba Betta Edu kaɗai ba ce da hannu a wannan badaƙala.
Bai kamata Betta Edu ita kaɗai ta zama abar ɗaukar izina ba. Akwai wadanda suka ci moriyar wannan kuɗaɗen da aka tanada domin talakawan Najeriya wanda su ma ya kamata a kama su, a bincike su kuma a gurfanar da su a gaban kuliya.”