✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da jihohi za su koma kayyade farashin kujerar Hajji — NAHCON 

Daga yanzu an daina biyan kuɗi bai daya da jihohi za su rika karɓa a wajen maniyyata.

Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana cewa daga yanzu gwamnatocin jihohi ne za su koma kayyade farashin kujerar hajji ga maniyyata sabanin bai ɗaya da ake biya a baya.

NAHCON cikin sabon tsari da ta fitar a wannan Talatar, ta ce jihohi ne za su kayyade cajin wasu kudaden da maniyyatan za su biya wanda zai fara aiki a Hajjin bana.

Hukumar ta yanke shawarar cewa a yanzu kowace jiha za ta kayyade farashinta bisa la’akari da wasu muhimman abubuwa na daiwainiya da alhazai kamar masauki da ciyarwa.

Ta ce daga yanzu an daina biyan kuɗi bai daya da jihohi za su rika karɓa daga wajen maniyyata.

Shugaban NAHCON, Jalala Arabi ne ya bayyana hakan a jawabinsa yayin ganawarsa da wakilan hukumomin alhazai na jihohi da kuma hukumomi masu zaman kansu a birnin Makkah da ke Saudiyya.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar NAHCON, Fatima Usara, ta fitar a ranar Litinin din da ta gabata, ta ce Jalal Arabi ya bayyana hakan a matsayin sabon matakin da aka dauka bayan ganawar da NAHCON ta yi da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya

A cewar sanarwar, Mista Arabi ya sanar da masu ruwa da tsaki cewa kowace jiha za ta daddale kan farashin masauki da ciyarwa domin sanin adadin kudin da maniyyata za su biya.

“Shugaban hukumar ta NAHCON ya sanar da taron cewa a bana kuɗin aikin Hajji ba zai kasance bai ɗaya ba, gwargwadon rahusar kuɗin masauki da abincin kowace jiha, gwargwadon kuɗin da maniyyatan za su biya,” in ji sanarwar.

NAHCON ta kuma kara karfafa wa jihohi gwiwa da su “yi amfani da wannan dama wajen ƙulla harkalla da ’yan kasuwa nagari domin samar wa alhazansu masaukai da abinci masu inganci.”