✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An naɗa ɗan shekaru 34 Firaminista a Faransa

Ya kasance mutum na farko dan luwaɗi a bayyane da zai riƙe wannan muƙamin.

An naɗa matashi Gabriel Attal mai shekaru 34 a matsayin sabon firaiministan Faransa, wanda shi ne mutum mafi karancin shekaru a tarihin Faransa da ya riƙe mukamin.

Wannan da na zuwa ne a ƙoƙarin shugaba Emmanuel Macron na farfado da gwamnatinsa domin inganta ayyukan gwamnatinsa.

Mista Attal ya maye gurbin Elisabeth Borne wadda ta yi murbus bayan watanni 20 a kan kujerar.

Elisabeth Borne tare da Shugaba Emmanuel Macron

A tsawon lokacinta, ta yi fama da rashin rinjaye a majalisar dokokin ƙasar, inda a bayan nan wasu rahotanni ke cewa ta yi murabus din  ne saboda rashin goyon bayan sauye-sauyen da shugaba Macron ke yi a gwamnatinsa.

Gabriel Attal, wanda a yanzu haka shi ne ministan ilimin Faransa zai jagoranci gwamnati a yayin da ake shirin zaɓen ’yan majalisar dokokin Turai a cikin watan Yuni.

Ya kasance mutum na farko dan luwaɗi a bayyane da zai riƙe wannan muƙamin.

A zaɓen 2017 ne ya zama ɗan majalisar dokoki kuma ɗaya daga cikin ɗan ga-ni-kashe-nin Shugaba Macron.

A lokacin yana ɗan shekara 29, an ba shi muƙamin ƙaramin minista a ma’aikatar ilimi sannan a shekara ta 2020 ya zama kakakin gwamnati.

Bayan da shugaba Macron ya yi tazarce, sai aka naɗa shi ministan kasafin kuɗi kafin ya koma ministan Ilimi.