✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya za ta kafa kwamitin yaƙi da digirin bogi

Ana ta mayar da martani ga matakin da aka ɗauka a kan digiri dan Kwatano.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da aniyarta ta kafa wani kwamiti na musamman domin yakar ayyukan makarantun da ke bayar da digirin bogi.

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’arta, Ben Goong ya fitar a wannan Talatar.

Sanarwar ta ce kwamitin zai ƙunshi mambobi daga ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyi daban-daban masu ruwa da tsaki domin yi wa tufkar hanci kan badakalar digirin bogi da ta kunno kai a baya bayan nan.

A cewar Mista Goong, Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne zai kaddamar da kwamitin a wannan Talatar.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki bayan wani wakilin Jaridar Daily Nigerian, Umar Audu, ya yi binciken ƙwaƙaf kan yadda masana’antun digirin bogi ke cin karensu babu babbaka a Jamhuriyyar Benin da Togo.

Wakilin wanda ya yi bad-da-kama, ya bayyana yadda ya samu shaidar digiri cikin makonni shida kacal kuma ya shiga shirin nan na masu yi wa kasa hidima wato NYSC.

Audu ya bayyana yadda ya tuntubi wani dillalin sayar da shaidar digiri a watan Disambar 2022, kuma ya mallaki shaidar kammala digirin a fannin aikin jarida a watan Fabarairun 2023 daga jami’ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies da ke Kwatano a Jamhuriyyar Benin.

Aminiya ta ruwaito cewa, bullar wannan rahoton mai cike da ban mamaki ne ya yamutsa hazo a Najeriya da kawaye, inda mahukunta da masu ruwa da tsaki suka shiga martani, inda wasu ke guna-guni masu Allah wadai kuma na yi.

Binciken dai ya nuna yadda badakala ta yi katutu a tarin manyan makarantu marasa lasisi da ke bayar da shaidar digirin dai bai inganta ba a kasashen Afirka ta Yamma, lamarin da ke nan ya sanya Gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin dakatar da tantance shaidar digiri daga jami’o’in Jamhuriyyar Benin da Togo wanda har a wasu wuraren ake yi musu lakabi da ‘Digiri dan Kwatano’.

Daga bisani ma dai Minista Tahir Mamman ya ce za su faɗaɗa binciken har a wasu kwalejoji da manyan makarantu da ke sauran kasashen Afirka irinsu Ghana.