Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa a shirye take ta shiga wani sabon yajin aiki kan abin da ta kira gazawar gwamnati wajen cika alkawuran da aka cim-ma da ita.
Kungiyar ta ce ta bai wa gwamnati wa’adin ranar Talata 31 ga Agusta, 2021, ta tuntube ta, ko kuma ta tsunduma yajin aiki.
- Ganduje ya tsawaita wa’adin hutun dalibai a Kano
- Rayuwar dana kamar ta kowane dan Najeriya ce —Sanata Na’Allah
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai a ranar Lahadi.
A cewar Farfesa Osodeke, a yanzu gwamnati ta daina sauraron su domin kuwa ta ma daina amsa kiran wayarsu.
A watan Maris din 2020, ASUU ta tsunduma yajin aiki bayan rashin jituwa da ta samu da gwamnati kan kudaden da take bai wa jami’o’i da wasu tsare-tsaren albashi da alawus-alawus.
An janye yajin aikin ne bayan gwamnatin da ASUU sun sanya hannu kan wata yarjejeniya domin biya wa kungiyar bukatunta, abin da ya ba da damar yanje yakin aikin a ranar 24 ga Disamba, 2020.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, har yanzu gwamnatinn ba ta gama cika bangarenta ba a yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar malaman jami’ar.