✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Arewa ta fi ko’ina hatsari a Najeriya —Sarkin Musulmi

’Yan bindiga sun koma bin gidaje suna daukar mutane ba yada aka iya da su.

Mai Alfarma Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce Arewacin Najeriya ne wuri mafi hadarin rayuwa a fadin kasar.

Sarkin Musulmi ya ce ’yan bindiga sun koma bin gida-gida suna garkuwa da mutane har mutane kan ajiye kadara domin su fanshi kansu da dukiyar.

Ya bayyana matukar damuwa cewa hauhawar farashi kayan abinci ya kai matakin da abinci ke neman gagarar mutane da yawa a Najeriya.

“Matsalar tsaro ta addabe mu, yanzu masu garkuwa sun koma bi gida-gida, kwanan nan sun shiga manyan makarantu a Zaria suka dauke mutane” inji shi.

Ya ce mutane a Arewa maso Yamma ba sa iya barci, ko a ranar Laraba ’yan bindiga sun kone wani kauye kurmus a Jihar Sakkwato.

“Rashin tsaro a Arewa ya sa mutane na tsoron tafiya daga Funtua zuwa Zariya wanda bai wuce kilomita 48 zuwa 50 ba; ba ma a maganar Sakkwato zuwa Abuja ko Kano.

“Mu muka san halin da muke ciki, Arewa na cikin rashin tsaro, sai kashe mutane ake yi.

“Yanzu mutane kan ajiye abubuwa a gida da za su ba wa ’yan bindiga su fanshi kansu idan ’yan bindigar sun kawo hari.

“A makonnin baya mutum 76 ’yan bindiga suka kahse a rana guda a Sakkwato. Ni da gwamna mun je wurin da abin ya faru a Gabashin Sakkwato.

“Labarin abubuwan da ke faruwa a Arewa ne ba sa yaduwa saboda ba mu da kafafen yada labarai da za su yayata abubuwan da ke faruwa yadda yakama shi ya sa; amma ba yadda ake tunanin cewa akwai tsaro a Arewa ba.

“Ko kadan ba tsaro a Arewa; ita ce ma wuri mafi hadari a kasar nan; ’yan bindiga na yawo a kauyuka dauke da AK47 ba wanda ke iya cewa uffan. A haka suke shiga kasuwanni su yi sayayya har su karbi canji”, inji shi.

Sarkin Musulmi ya yi jawabin ne ga taron Majalisar Addinai ta Kasa (NIREC) a Abuja ranar Alhamis.

Tashin farashin kayan abinci

Sarkin Musulmi ya bayyana damuwa game da tashin gwauron zabo da kayan masarufi musamman kayan abinci ke yi a Najeriya.

Basaraken ya koka cewa yananin ya kai kayan abinci ba sa tabuwa a wurin da dama daga cikin ’yan Najeriya.

“Farashin kayan abinci ya tashi sosai don haka dole mu dauki mataki.

“Saboda tsada, yanzu albasa ta fi karfin mutane da yawa; yunwa na iya haifar da abin da ba a yi zato ba.

“Tsadar albasar a Najeriya a yau alama ce ta halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki”, inji Sarkin Musulmi.

“Ya kamata mu zauna a tsanake mu kalli wadannan batutuwa mu ba da shawarwarin magance matsalolin.

“Babban abin da muka rasa shi ne rashin aiwatar da matakai da kauce wa yin daidai, duk abin da za mu yi sai mun yi muna-muna”, inji Sarkin Musulmi.

Dole a shawo kan matsalar tsaro

Ya shaida wa taron cewa wajibi ne hukumomi da ’yan kasa sun rika yin abin da ya kama domin babu yadda za a rika yin abin da aka ga dama a kasa kuma a yi tunanin kasar za ta gyaru.

“Wajibi ne mu bi doka. Mun ji wasu na kira da rusa rundunar ’yan sandan SARS kuma Shugaban Kasa ya yi hakan, amma daga baya mu da kanmu muka koma muna rokon ’yan sanda su dawo.

“Ba zai yiwu a ce babu ’yan sanda ko jami’an tsaro ba, duk lalacewarsu suna da rana.

“Abun da ake bukata shi ne a zakulo bara-gurbin cikinsu sannan a inganta hukumomin.

“Zagin ’yan sanda, sojoji ko sauran jami’an tsaro ba zai haifar mana da mai ido ba, da kasar za ta fada cikin rashin doka da gaba daya za mu shiga uku”, inji shi.

Shi ma da yake jawabi, Shguaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Dokta Samson Olasupo Ayokunle, ya koka game da hauhawar farashin kayan abinci da yadda hakan ke shafar jama’a.

Ya yi kira ga gwamnati da ta rika daukar mataki a kan abubuwa tun kafin su kazance.

Ayokunle wanda ke jagorantar NIREC tare da Sarkin Musulmi ya yi wa Allah godiya kan yadda ya kawo wa Najeriya sauki cikin annobar COVID-19 idan aka kwatanta da wasu kasashe.

Ayokunle ya yi kira ga al’ummomin Musulmi da Kiristoci da su tashi tsaye wurin yakar matsalar fyade da ke addabar al’umma.