Kwamitin Gudanarwar APC na kasa ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya martaba hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan batun daina amfani da tsofaffin takardun kudi.
Wannan kira dai na zuwa ne yayin wani taro da gwamnonin jam’iyyar da shugabanta na kasa, Sanata Abdullahi Adamu suka gudanar ranar Lahadi a Abuja.
- NAJERIYA A YAU: Shin don talakawa gwamnoni ke adawa da canjin kudi?
- Tsohon Shugaban PDP a Kano ya sauya sheka zuwa NNPP
A taron wanda aka shafe tsawon sa’a biya ana tattaunawa, ya kara nuna yadda APC ta tsunduma cikin rudani da rabuwar kawuna, inda shugabancin jam’iyyar ya bi sahun wasu gwamnonin kasar da ke fito-na-fito da manufar daina karbar tsoffin kudi ta Shugaba Buhari.
A cewar Kwamitin, “Muna kira ga Babban Ministan Shari’a na Tarayya da Gwamnan Babban Bankin Najeriya da su mutunta umarnin Kotun Koli na wucin gadi wanda har yanzu ke gabanta.
“Taron yana kira ga Shugaba Buhari da ya sa baki wajen warware matsalolin da canjin kudin ya haifar wa ‘yan Najeriya.”
A hukuncin da Kotun Koli ta zartar, ta dakatar da wa’adin da CBN ya bayar na daina amfani da tsofaffin takardun kudi na 200, 500 da 1000 daga ranar 10 ga watan Fabrairu.
Sai dai duk da wancan hukunci na Kotun Koli, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya tabbatar da cewar wancan hukunci na daina amfani da kudin yana nan daram.
Kazalika, a ranar Alhamis din da ta gabata ne, Shugaba Buhari ya kara wa’adin ci gaba da amfani tsohuwar takardar Naira 200 har na tsawon wata biyu.
Sai dai wasu daga cikin gwamnonin APC da suka hada da Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna da Yahaya Bello na Kogi da Bello Matawalle na Zamfara da Abdullahi Umar Ganduje na Kano da kuma takwaransu na Ogun, Dapo Abiodun, sun kalubalanci umarnin na Shugaban Kasa.
Yayin gana wa gwamnonin jam’iyyar, shugaban na APC ya goyi bayansu inda ya koka kan irin wahalar da canjin kudin ya haifar.
Canjin kudin dai da CBN ya yi, ya bar baya da kura inda wasu ‘yan siyasa ke ganin da gan-gan aka fito da shi don kawo musu zagon-kasa a zaben 2023 da ke tafe.
Yayin da a gefe guda kuma, tsarin ya haifar da tashin-tashina a wasu jihohin da zanga-zanga ta barke, tare da kai hare-hare kan bankuna da masu sana’ar PoS.
Tuni dai miliyoyin mutane suka koka tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba halin da suke ciki, yayin da wasu kuma ke zargin tsarin na barazana da durkushewar kasuwancinsu.