Mai Bai Wa Gwamnan Sakkwato Shawara kan Harkokin Karkara, Malami Muhammad Galadanchi (Bajare), ya bai wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar, kyautar Naira miliyan 22 domin gudanar da shagalin Sallah Karamar.
Yayin bayar da kyautar a ranar Alhamis, Bajare ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiyarsa ga jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, da Gwamna Ahmad Aliyu, bisa damar da suka ba shi don ba da gudunmawarsa ga ci gaban jihar.
“Wannan tallafi saƙon godiya ne daga shugabanninmu zuwa gare ku. Idan ba su ba mu dama ba, ba za mu iya wannan ba.
“Kuma muna shirye mu ƙara tallafawa a duk lokacin da buƙata hakan ta taso,” in ji shi.
Ya jinjina wa al’ummar Ƙaramar Hukumar Sakkwato ta Arewa, bisa sadaukarwar da suka yi wajen ganin jam’iyyar APC ta yi nasara, inda ya ce hakan ne ya sa suka cancantar a yi masu hidima.
Bajare, ya tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafa wa magoya bayan jam’iyyar lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da ci gaban tafiyar siyasarsu.
Dangane da tsarin rabon tallafin, ya ce kowane mutum da aka zaɓa zai amfana da kuɗi tsakanin Naira 100,000 zuwa miliyan ɗaya, ya danganta da matsayinsa.
Haka kuma ya yi fatan al’umma za su gudanar da shagalin sallah cikin lumana da kwanciyar hankali.