✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata ranakun hutun sallah

Ministan ya taya al'ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar sallah.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba.

Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan.

Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma.

Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaban ƙasa.

Ya yi fatan cewa bukukuwan salla za su ƙara haɗin kai tsakanin mutane duk da bambancin addini da ƙabilanci da ake da su.

Haka kuma, ya yi kira ga jama’a da su yi bukukuwan ta hanyar tunawa da mabuƙata, ta yadda za a taimake su.

A madadin Gwamnatin Tarayya, ministan ya aike da saƙon fatan alheri ga dukkanin Musulmi tare da addu’ar Allah Ya sanya farin ciki a zukatan kowa.